Limamin Tehran: Al'umar Iran Ba su Gaskata Kowace Gwamnati Ta Amurka.

  • Lambar Labari†: 791284
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Al'ummar Iran bata dogaro da kowace gwamantin Amurka

Wanda ya jagoranci Sallar juma'ar Tehran ya ce; Al'ummar Iran ba su taba gaskata  siyasar kowace gwamnati ta Amurka ba.

Ayatullah Ahmad Khatami ya fada a cikin hudubarsa ta sallar juma'a cewa; Sakamakon da zaben Amurka ya zo da shi, baya nufin samun sauyi a cikin siyasar kasar na nuna karfi akan al'ummar wannan yankin.

Ayatullah Ahmad Khatami ya ci gaba da cewa; Al'ummar ta Iran ba za su taba mika kai ga manufofin Amurka ba.

Bugu da kari, Ayatullah Ahmad Khatami ya ce; Al'ummun kasashen duniya sun gaji da yadda Amurkan ta ke tsoma baki a harkokin cikin gidansa, saboda haka abinda ya fi dacewa ga shugaban kasar ta Amukra shi ne ya maida hankali wajen waraware matsalar mutanen kasarsa.

Limamin na Tehran ya ce idan har sabon shugaban kasar ta Amurka yana son ya aikata abinda magabatansa su ka yi, to shi ma zai bi sawunsu ya zama wanda ake ki a duniya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky