Iran Ta Hanawa 'Yan Majalisar Amurka Visa

  • Lambar Labari†: 759048
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Iran ta yi watsi da bukatar bada takardar izinin (visa) ga wasu 'yan majalisar dokokin Amurka na republican guda uku dake son shiga kasar domin duba halin da ake ciki dangane da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da Iran.

Da yake maida martani akan wannan bukata cikin wata wasika, ministan harkokin wajen Iran Muhammad Javad Zarif, ya ja kunnan Amurka akan duk wani yunkurin ta, na neman canza batutuwan da yarjejeniyar da aka cimma da mayan kasashen duniya.

'Yan majalisar dokokin dake bukatar izinin visa din sun hada da Mike Pompeo, Lee Zeldine da Frank Lobiondo.

Mr Zarif ya kara da cewa babu wani dan majalisa ko dan wata kasa memba a mayan kasashen 5+1 dake da incin sanya ido kan Iran akan yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da ita, sannan majalisar Amurka bata da wani hurimi na gayawa kasashen duniya abunda zasu yi.

Don haka a cewar Mr Zarif hukumar kula da makamashin nukiliyar ta duniya ce kawai keda incin sanya ido ko kuma canja abunda yarjejeniyar ta kunsa.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky