Ayatollah Khamenei: Ba Za Mu Taba Amincewa Da Amurka Da Salon Yaudararta Ba

  • Lambar Labari†: 758004
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa, ba su taba yarda da Amurka ba, sakamakon irin cutarwar da ta yi wa kasar Iran a tsawon tarihi, musamman ma bayan samun nasarar juyin juya halin muslunci shekaru 37 da suka gabata.

Jagoran ya bayyana hakan ne ne yau a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban dubban daruruwan mutane a hubbaren marigayi Imam Khomenei, a taron da ake yi na cika shekaru 27 da rasuwarsa, taron da ke samun halartar mutanen kasar ta Iran daga dukkanin larduna, da kuma baki 'yan kasashen ketare.

 Ayatollah Khamenei ya ce dadin bakin Amurka yaudara ce, inda ya buga misali da yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da Iran da kuma manyan kasashen duniya, inda ya ce sauran bangarorin tattaunawr sun yi aiki da wannan yarjejeniya, amma Amurka har yanzu ba ta aiwatar da ita, wanda hakan ya kara tababtar musu cewa ba a aminta da ita.

Ya kara da cewa dukaknin gwagwarmayar da marigayi Imam Khomenei ya yi, sakamako ne na danniya da zaluncin da Amurka take yi a kan al'ummomi raunana, wanda kuma sakamakon gwagwarmayar Imam Khomeni, Iran ta fita daga karkashin kama karya da mulkin mallakar Amurka.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky