Ruhani: Isra'ila Ce Za Ta Amfana Da Kafar Ungulun Da Saudiyya Take Wa Aikin HajjiRuhani: Isra'ila Ce Za Ta Amfana Da Kafar Ungul

  • Lambar Labari†: 757463
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana cewar kafar ungulun da kasar Saudiyya ta yi da ya kai ga hana mutanen Iran zuwa aikin hajjin bana wani lamari ne da zai amfani haramtacciyar kasar Isra'ila da manufofinta a yankin Gabas ta tsakiya.

Shugaba Ruhani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a lardin Azarbaijan ta yamma inda ya ce: Kokarin da mutanen da suke kiran kansu masu kula da Masallatai biyu masu tsarki na musulmi na yin kafar ungulu ga tafarkin Ubangiji da kuma aikin Hajji bugu da kari kuma kan haifar da rikici da rashin tsaro a yankin nan, wani kokari ne kawai na biyan bukatu da manufofin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Shugaba Ruhani ya kara da cewa: Aikin Hajji, haka nan garin Makka da Madina na dukkanin musulmi ne sannan kuma wasu fagage ne na cimma manufofin musulmin duniya. Shugaban ya kara da cewa: babbar manufar sahyoniyawan duniya da sauran ma'abota girman kai ita ce yada ta'addanci da zubar da jini wanda hadin kai da tsayin dakan al'ummar Iran ya kawo musu cikas wajen cimma wadannan bakaken manufofinsu, wanda hakan shi ne ummul aba'isin din irin kiyayyar da suke da al'ummar Iran.

A shekaran jiya ne dai ministan al'adu da shiryarwar Musulunci ta kasar Iran Ali Jannati ya sanar da cewa al'ummar Iran ba za su tafi aikin hajji na bana ba sakamakon kafar ungulun da Saudiyya ta yi na hana maniyyatan na Iran zuwa aikin hajjin na bana.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky