Ganawar Jagora da Iyalin Shahid Mustapha Badruddin

  • Lambar Labari†: 756685
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana tsohon babban kwamandan dakarun kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Shahid Mustafa Badruddeen a matsayin wani jarumi kana kuma tsayayyen dan gwagwarmaya don haka yayi masa fatan samun karin matsayi da daukaka a wajen Allah Madaukakin Sarki.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi a yammacin jiya da iyalan Shahid Badruddeen din da suka kai masa ziyara a gidansa da ke nan birnin Tehran, inda yayin da yake jinjinawa irin jaruntakar da shahidin ya nuna ya bayyana cewar inda da labarin irin jaruntakar da wannan babban shahidi ya nuna, a saboda haka ina roka masa samun karin daukaka a wajen Allah, kamar yadda kuma na ke roka muku, a matsayinku na iyalansa karin hakurin wannan rashin.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar kasar Labanon albarkacin kasantuwar kungiyar Hizbullah da dakarun gwagwarmaya ta zamanto wata kasa abar misali, da kuma tasiri duk kuwa da rashin girma da fadin kasa da take da shi, wanda ya ce hakan ya samo asali ne albarkacin tsayin dakan dakarun na Hizbullah da kuma jinin shahidan da ya zuba.

A ranar 13 ga watan Mayu din nan kungiyar Hizbullah din ta sanar da shahadr shahid Badruddeen sakamakon wani hari da 'yan ta'adda suka kai wa daya daga cikin cibiyoyin kungiyar da ke kusa da babban filin jirgin saman Damaskus, babban birnin kasar Siriya288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky