Kasar Iran Ta Yi Tofin Allah Tsine Kan Sama Da Fadi Da Dukiyarta Da Amurka Ta Yi

  • Lambar Labari†: 750938
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Limamin da ya jagoranci sallar Juma'a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran yayi tofin Allah tsine kan matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na kwashe kudaden ajiyar Iran kimanin biliyan biyu tare da jaddada wajabcin dawo da kudaden.

A hudubar sallarsa ta jiya  a babban Masallacin birnin Tehran na kasar Iran; Ayatullahi Ahmad Khatami ya mai da kakkausar martani kan matakin da kotun kolin kasar Amurka ta dauka na rike kudaden Jamhuriyar Musulunci ta Iran kimanin dalar Amurka biliyan biyu, yana mai jaddada cewa; Mahukuntan Iran ba zasu taba amincewa da wannan bakar siyasa ba, don haka dole ne su bi duk matakan da suka dace wajen dawo da dukiyar al'ummar kasarsu.

Har ila yau Ayatullahi Khatami ya mai da martani mai gauni kan matakin da wasu daga cikin mahukuntan Saudiyya da suke kula da ayyukan hajji ke kokarin dauka na hana al'ummar Iran zuwa aikin hajjin bana; Yana mai cewa; Makkah da Madinah wajaje ne masu alfarma kuma mallakin addinin Musulunci ne da dukkanin al'ummar musulmin suke da hakkin ziyartarsu, don haka babu wani masaraucin da ke da hakkin hana al'ummar Iran ziyartarsu domin gudanar da ayyukan ibadu.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky