Shugaba Zuma Ya Gana Da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci

  • Lambar Labari†: 749658
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Aya. Sayyeed Aliyul Khamniae ya gana da shugaban kasa

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Aya. Sayyeed Aliyul Khamniae ya gana da shugaban kasar Afrika ta Kudu Jorcob Zuma wanda ya fara ziyarar aiki a nan Tehran.

A ganawar jagoran ya bukaci kasashe masu 'yenci su hada kai don kawu ci gaba a tsakaninsu duk tare da matsaloli wadanda manya manyan kasashen duniya suke haddasawa a wannan fagen. Jagoran ya bayyana cewa danganta tsakanin kasashen biyu tana da kyau tun da dadewa kuma yakama a kara karfafata.

A nashi bangaren shugaban kasar Afrika ta Kudu Jocop Zuma ya bayyana cea gwamnatinsa bata amince da takunkuman da kasashen yamma suka dorawa Jumhuriyar musulunci ta Iran kan shirinta na Nuklia ba, kuma yanzun tunda an dauke takunkuman yana fatan kasashen biyu zasu kara hada kai don fadada dangantakan da ke tsakaninsu a dukkan bangarori.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky