Ruhani: Iran Ce Ta Hana Yaduwar Ayyukan Ta'addancin Kungiyar Da'esh

  • Lambar Labari†: 749400
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin ja gabar fada da ta'addanci, yana mai cewa kokarin Iran shi ne ya dakile yaduwar ayyukan kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS) a yankin gabas ta tsakiya.

Shugaba Ruhani ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a wajen wani taron kasa da kasa kan yanayin, addini da kuma al'adu da aka gudanar a nan Tehran inda ya ce da ba don kokarin Iran ba da kuwa kungiyar Da'esh ta sami damar ci gaba da cin karenta babu babbaka da kuma cimma manufarta da tabbatar da ikonta gaba daya a kasashen Iraki da Siriya. Don haka ya ce wajibi ne a jinjina wa al'ummar Iran saboda wannan kokari da suka yi na fada da ta'addanci.

A wani bangare na jawabin nasa, Shugaba Ruhani yayi watsi da farfagandar da wasu kasashe suke yadawa na cewa Iran tana barazana ga zaman lafiyan yankin Gabas ta tsakiya inda ya ce tsawon karnoni biyun da suka gabata al'ummar Iran ba su taba kaddamar da yaki akan wata kasa ba, to amma lalle za su tsaya kyam wajen fada da duk wani kokarin wuce gona da iri a kansu don kare kasarsu.

A safiyar yau Asabar ne aka bude taron kasa da kasa kan yanayin, addini da kuma al'adu karo na biyu a nan Tehran wanda kuma ya samu halartar jami'ai da masana daga kasashe daban-daban na duniya.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky