Iran Ta Kirayi Gwamnatin Amurka Da Ta Daina Goyon Bayan Ayyukan Ta'addanci

  • Lambar Labari†: 746419
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Ministan Tsaron Iran Ya Kirayi Gwamnatin Amurka Da Ta Daina Goyon Bayan Ayyukan Ta'addanci

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da zargin sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry na cewa tana barazana ga tsaron yankin Gabas ta tsakiya tana mai cewa wajibi ne Amurka ta daina goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda sannan kuma ta fice daga yanki matukar dai tana son taimakon tsaron yankin ne.

Ministan tsaron kasar ta Iran Birgediya Janar Husain Dehqan ne ya bayyana hakan a wata ganawa da yayi da manema labarai inda ya ce: "matukar da Amurkawa suna son tabbatar da tsaron Gabas ta tsakiya ne, to wajibi ne su fice daga yankin sannan kuma su daina goyon bayan 'yan ta'addan da suke ci gaba da zubar da jiinin al'ummomin yankin.

Janar Dehqan dai yana mayar da martani ne ga kalaman sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry na kwanakin baya inda ya zargi Iran da zama barazana ga tsaron yankin Gabas ta tsakiya. Janar Dehqan ya kara da cewa Idan da John Kerry ya yi tunani ko da na minti guda ne kan wannan lamari, to da kuwa bai fadi irin wannan magana ta wauta da rashin mafadi ba.

A wani bangare na jawabin nasa, ministan tsaron na Iran ya ce jami'an Amurka suna fadin irin wadannan maganganu ne don tsoratar da kasashen yankin Gabas ta tsakiya don su ci gaba da dogaro da su da kuma sayen makamansu. Yana mai cewa irin wadannan maganganu suna nuni da irin yanke kaunar da Amurka ta yi ne wajen dakatar da shirin kare kai na Iran.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky