Rauhani Ya Aike Da Sakon Ta'aziyya Ga Gwamnatin Pakistan

  • Lambar Labari†: 744032
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Shugaba Rauhani Ya Aike Da Sakon Ta'aziyya Ga Al'uma Da Gwamnatin Pakistan

Shugaban kasar Iran Sheikh Hassan Rauhani ya aike da sakon ta'aziyya zuwa ga gwamnati da kuma al'ummar kasar Pakistan, sakamakon harin ta'addancin da aka kai a birnin Lahore.

A cikin sakon da Shugaba Rauhani ya aike wa Firayi ministan kasar Pakistan, ya bayyana takaicinsa matuka dangane da kisan fararen hula da 'yan ta'adda suka yi suka yia kasar ta hanyar tayar da bam a Lahore, tare da yin ta'aziyya ga gwamnati da kuma dukkanin al'ummar kasar musamman ma iyan wadanda abin ya shafa.

A ranar Lahadi da ta gabata ce dai 'yan ta'adda masu akidar kafirta musulmi suka tayar da bama-bamai a wani wurin wasan yara, inda suka kashe mutane fiye da 70 tare da jikkata wasu fiye da 300.


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky