Hare-haren sojoji a Zariya - Sojoji sun hana a yiwa gawwakin da suka kashe sutura

  • Lambar Labari†: 724990
  • Taska : Harkar musulunci a Nageria
Brief

Da farko bayan kisan rashin tausayi da sojojin gwamnatin Nigeria suka yiwa al'ummar musulmi 'yan uwa a Zariya, a wurare daban daban, a Husainiyar Baqiyyatullah da gidan jagoran Harkar Musulunci a Nigeria dake unguwar Gyallesu sai kuma a lokaci guda suka hana isa don a dauko gawwawakin ayi musu sutura kamar yadda

Addinin musulunci ya koyar.

Sai daga baya bayan da jami'an kula da bada agaji na gaggawa na RED CROSS suka iso sannan ne suka shiga tsakani.

Haka nan kuma da yawa daga cikin wadanda suka harba da farko ba su riga sun cika ba, amma saboda rashin bada dama a dauki mataki na gaggawa yasa sun yi ta zubar da jini har suka karasa cikawa.

Kada mu manta hatta shi shugaban bangaren bada agaji na Harkar Musulunci watau ISMA Dr Mustafa Ummar rahotanni sun tabbatar da sojojin sun bishi sun kashe.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky