Rauhani; takunkumi ba zai yi tasiri ga Iran ba

  • Lambar Labari†: 680939
  • Taska : ABNA
Brief

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S}-abna-Hujjatul islam walmusilimin Hassan Rauhani yayin da yake Magana da al’ummar kasar ta gidan talabijin kai tsaye ya bayyana cewa, al’umma kasar Iran ta nunawa Duniya cewa takunkumi da takurawa ba zaiyi nasara wurin kawar da kasar a shirinta na makamashin Nukiliya ba.
A cigaba da jawabin sa ya yabawa jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khamna’I a bisa goyan bayan da ya ba wakilan kasar a yayin da suke tattaunawa da takwarorin aikin su na kasashen 5+1.
Rauhani yace; aiyukan fasaha na makamashin Nukiliya hakkin Iran ne sannan kuma dole ne a cirema kasar duk wani takunkumi da aka kakafamata.
A jiya ne kasar Iran da kasashen 5+1 suka rattafa hanun akan a mincewa da aiyukan makamashin Nukiliya na zaman lafiya na Iran.ABNA


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky