• An yi taron tunawa da ranar Kudus ta duniya da kuma kaddamar da littafi a Abuja

  A yau Asabar,29 ga watan Yuli 2017,’yan harkar Musulunci a Nigeriya suka shirya taro na musamman domin tunawa da ranar Kudus ta duniya da kuma kaddamar da littafi a Abuja tarayyan Nigeriya. An yi wannan taro ne dakin taro na Merit House dake Abuja.Bayan bude taro da addu’a ne,Dr Shu’aibu ya bayyana maqasudin taron da taken taron da kuma mutanen da zasu gabatar da kasida a wajen taron. Hon.Ebenezer Oyintikin,daya daga cikin wa’yanda suka gabatar da kasida a wajen ya bayyana cewa shi kirista ne amma yana amfani da wani hadisi ya samu daga Annabi Muhammadu(sawa) cewa: “Idan abinda zaku saya ma ‘ya’yanku ba zasu isa ku raba ku hada da yaran makwabtanku ba,to,ku basu a cikin gida kar ku sake su fita dashi waje.” Ya cigaba da cewa ya san Harkar Musulunci wadda Sheikh Zakzaky yake jagoranta ta doru ne akan wannan hadisi na Annabi da tsari na tausayi ga al’umma da jin kai. Shi kuma Hon.Deji Adeyanju a nashi jawabin cewa yayi: “Ban taba ganin lalatacciyar gwamnati kamar ta Nigeriya ba.Basa girmama mutanen kirki masu ilimi amma suna sasanci da lallaban ‘yan ta’adda.Na tabbata da shi’a suna da makamai da tuni gwamnati ta fara sasanci da su. “Takurawar da gwamnati take maku ta kaikace tana fada maku ne ku dauki makamai ku zama ‘yan ta’adda,sai ku kuma kuka nuna masu kuna da hankali da tunani.” Deji ya nuna takaicinsa dangane da lalacewan kasan nan,yana cewa: “Ya gwamnati zata kashe mutum sama da 1000 amma shugaban kasa ya fito gidan talabijin yana cewa “me yasa suke dukan kirjin soja?”Wallahi baka da Kalmar da zaka iya fassara wannan gwamnati.” Dr John Danfulani a lokacin da yake gabatar da nashi bayanin ya bayyana abubuwan alkairi da ya gani game da Harkar Musulunci a Nigeriya,yana cewa: “Na halarci ayyukan da tarukan IMN da yawa fiye da yadda wani dan IMN din.Na je Tattakin Arba’een,na ga bayin Allah da aka kashe a lokacin tattakin,na ziyarci Sheikh Zakzaky lokaci daban daban.Na fahimci cewa ‘yan harka suna da tsari kuma suna tare da Allah.Ya za a yi cikin kasa da shekara 40 ya zama an iya samar da mutane sama da miliyan 20 in ba abin Allah ba? “Kaman yanda na ga wani hadisi yana cewa shi mutum imma dan uwanka ne a halitta ko dan uwanka a addini.Kuma shi’a sun yi riko da wannan hadisin ta yanda suke mu’amala da kowa kamar yadda ya gabata.Har yanzu ba zaka taba samun dan shi’a dan ta’adda ba,dukkan bangarorin ISIS,DAESH da Boko Haram dukkansu ba shi’a bane.” Daga cikin wa’yanda suka gabatar da kasida a wajen taron akwai;Professor Chidi Odunkalu,Alhaji Muktar Sirajo,da sauransu. Sheikh Abdulhamid Bello ne ya wakilci Sheikh Yakubu Yahaya Katsina a taron.Sannan da aka zo kaddamar da littafin da aka wallafa,sun sayi kofi biyu akan kudi naira dubu dari ga Sheikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah Ibrahim. Sannan Ahlul Dothour sun sayi kwafi 10 akan kudi naira dubu dari biyu,sai Malam Gamawa ya sayi kwafi 10 akan kudi naira dubu dari biyu da hamsin ga Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Nasiru ElRufa’I da Sufeto Janar na ‘yan sanda da sauransu. Duk da ‘yan sanda sun kawo ziyara wajen sun tafi ba tare da wani abu ya faru ba,kuma an kammala taron lafiya cikin nasara.

  cigaba ...
 • Hizbullah: 'Yan Ta'adda Na Shakar Lumfashinsu Na Karshe A Gabashin Lebanon

  Mayakan kungiyar Hizbullah na ci gaba da killace 'yan ta'adda da suka yi saura a cikin yankin Ta'al Nisab da ke cikin gundumar Jurud Arsal a kan iyakokin Lebanon da Syria, inda dakaruna na Hizbullah suka bayar da wa'adi ga 'yan ta'addan takfiriyyah da su mika kansu da makamansu, ko kuma a murkushe su da karfin bindiga.

  cigaba ...
 • Jami’an tsaro sun tarwatsa masu taron tunawa da Shahidan Quds 2014

  A yau ne da gamayyan jami’an tsaron da suka hada da Mopol da ‘yan sanda da sojoji suka zo farfajiyar filin Darur Rahma dake a kan hanyar zuwa Jos a lokacin da ake yin taro domin tunawa da ‘yan uwa almajiran Sheikh Zakzaky da sojoji suka kashe a Muzaharan Quds ta 2014 suka umurci kowa da kowa da ya watse a ya bar wajen. Jami’an tsaron da suka je Darur Rahma domin tarwatsa masu wannan taro sun kai kimanin mota 8 zuwa 10 dauke da muggan makamai suna umartan mahalarta taron da su bar wajen taron. Ganin haka ya sanya jagororin taron suka yi addu’a suka ziyarci shahidan dake kwance a wajen,sannan suka fito daga wajen cikin natsuwa,su kuma jami’an tsaron gefe guda suna bin su a baya har suka fito bakin titi suka hau ababen hawansu suka tafi suka bar wajen. A lokacin da majiyarmu ta tuntubi AC din Zariya,ACP Ibrahim akan ko me yasa jami’an tsaro suka je wajen wannan taro domin su hana shi?Sai yace : “akwai matsala ne a wajen shi yasa suka basu shawara su bar wajen.” Shi kuma Sheikh Abdulhamid Bello,daya daga cikin jagororin wannan taro cewa yayi: “Mun saba duk shekara muna shirya irin wannan taro domin tunawa da ‘yan uwanmu su 34,ciki har da ‘ya’yan jagoranmu guda uku da aka kashe a shekarar 2014. “Mun fara taron da karfe 8:00 na safe,can wajen karfe 10:00 na safe sai ga jami’an tsaro sun zo sun same mu,da farko sun fara zagaye mu ne ba tare da sun ce komai ba,sai muka cigaba da taron mu. “Zuwan ‘yan sanda karkashin jagorancin ACP ked a wahala,sai suka fara kawo mana cikas a taron,sun ta kokarin su sa mu harzuka amma ba suyi nasara ba.Sai suka zo suka cewa mai wa’azi ba damuwa,yi ka gama ka karkare ku tashi ku bar wajen.” Sheikh Bello ya sheda ma majiyarmu cewa taron ya samu halartan almajiran Sheikh Zakzaky daga garuruwan kusa da nisa kuma anyi jawabai masu yawa kafin zuwan jami’an tsaro su kawo cikas

  cigaba ...
 • An Gabatar Da Muzaharar Lumana A Abuja

  A jiya laraba ne, matasa karkashin dandamalin daliban harkar musulunci na Nigeriya suka gudanar da muzaharan lumana a garin Abuja, domin neman gwamnatin Nigeriya ta bi umurnin kotu ta saki jagoransu Sheikh Ibrahim Zakzaky wanda yake a tsare a hannun DSS tun Disambar 2015 duk da babban kotun tarayya tayi umurni da sake shi a watan Disambar 2016. In ba a manta ba sojoji a lokacin da suka kai wannan hari a gidan Sheikh Zakzaky dake Zariya sun harbi malamin a wurare da dama na jikinshi wanda yayi sanadin rasa idonsa daya.Sannan an kashe masa 'ya'ya uku tare da harbin mai dakinsa a qugu. Wadannan matasa dalibai sun gudanar da wannan muzaharan cikin tsari,suna dauke da kwalaye an rubuta free zakzaky, suna wake na neman a saki jagoransu,suna tafiya har zuwa inda zasu kulle muzaharan,kawai sa 'yan sanda suka zo suka fara antaya masu tiyagas. Har zuwa lokacin hada wannan labarin bamu da labarin kama wani daga cikin masu muzaharan ko samun rauni daga cikinsu. Kuna iya ganin wasu hotunan muzaharan a kasa:

  cigaba ...
 • Ana yunkurin hallaka Sheikh Zakzaky

  Shugaban dandalin yada labarai na harkar musulunci a Nigeriya,Ibrahim Musa ya fadi a wata takarda ta manema labarai da ya aiko da ita yau 19 ga watan 2017 cewa an yunkurin hallaka jagoran harkar musulunci a Nigeriya.Yana cewa:

  cigaba ...
 • Martanin Iran Kan Sabbin Takukuman Amurka

  Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta mayar da martani dangane da sabbin takunkuman da Amurka ta dora ma wasu kamfanoninta da kuma wasu jami'an kasar, dangane da shirin Iran na kera makamai masu linzami na ballastic.

  cigaba ...
 • Zamu daukaka kara Inji Sheikh Yakubu Yahaya Katsina

  Sheikh Yakubu Yahaya Katsina ya bayyana cewa zasu daukaka kara dangane da hukuncin da Alkalin babban kotun tarayya na Kaduna yayi na watsi da karar da Sheikh Ibrahim Zakzaky ya shigar a kotun yana neman haqqoqinsa a kotun.

  cigaba ...
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky