• Dakarun IRGC Na Iran Sun Sanar Da Shirin Daukar Fansa Kan 'Yan "Da'esh"

  Kakakin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran (IRGC) Birgediya Janar Ramazan Sharif ya bayyana cewar za su dau fansa kan kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS) sakamakon kisan gillan da suka yi wa daya daga cikin dakarun kare juyin da suka kama a kasar Siriya ta hanyar yi masa yankan rago.

  cigaba ...
 • Ministan Yada Labaran Nigeriya da Femi Adesina da Malam Garba Shehu Sun Ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari a Ingila

  Femi Adesina a wata takarda da ya fitar yau Asabar,12 ga watan Agusta 2017,ya bayyana cewa yana cikin tawagar Ministan Yada labarai,Mr Lai Muhammad da suka kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara a Ingila. A lokacin da Shugaba Buhari yake masu bayani dangane cigaban da ya samu dangane da lafiyarsa ya bayyana masu cewa: "Alhamdulillah,na samu sauki sosai dangane da rashin lafiya ta,kuma ina son in dawo gida,amma dai na ga ya fi dacewa in bi umurnin likita na,ba wani ba saboda shike da cikakken masaniya dangane da abinda ya kamata na yi."in Shugaba Buhari. In ba a manta ba,Shugaba Buhari ya kwashe fiye da kwanaki 90 a Ingila domin ganin likitansa,wanda wannan ya haifar da taqaddama tsakanin mutanen Nigeriya.

  cigaba ...
 • Hotunan zanga-zangar neman Buhari ya yi murabus

  Wasu kungiyoyin al'umma sun yi zanga-zanga suna kira ga shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ko dai ya koma aiki ko kuma ya sauka. A ranar Litinin ne wasu kungiyoyin al'umma suka yi zanga-zanga suna kira ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ko dai ya koma aiki ko kuma ya sauka. Masu zanga-zangar sun ce sun shirya ta ne ganin cewa shugaba Buhari ya shafe kwanaki 92 yana jinya a birnin London, kuma har yanzu babu wani bayani kan yanayin rashin lafiyarsa ko kuma lokacin da zai koma bakin aiki. Wani mawaki mai suna Charly Boy ne ya shirya zanga-zangar wacce ba ta samu halartar mutane da dama ba. Mutanen sun yi ta daga kyallaye da ke dauke da rubuce-rubuce da dama na neman shugaban ya sauka daga mulki. Gomman masu zanga-zangar sun faro ne daga dandalin Unity Fountain da ke birnin tarayya Abuja, inda suka dire a kwanar shiga fadar shugaban kasa, bayan da jami'an tsaro suka dakatar da su. Daga cikin kungiyoyin da suka halarci zanga-zangar har da kungiyar 'yan uwa Musulmai ta Shi'a da ke kira da a saki shugabanta Malam Ibrahim El-Zakzaky MAsu zanga-zangar dai sun ce za su ci gaba da yin zaman dirshan a wajen har sai sun ga abin da ya turewa buzu nadi

  cigaba ...
 • Rana Ta Uku:Bukin Tunawa Da Munasabar Haihuwan Imam Ali Ibn Musa Ar-Ridha a Kano

  Yau Asabar,5 ga watan Agusta 2017,ta zama ranar khatma na taron tunawa da munasabar haihuwan Imam Ali Ibn Musa Ar-Ridha da kuma sanya tuta a Hussainiyyar Kofar Waika Kano. In ba a manta ba,wannan taro na Ad-Da’iral Ammah ce wanda Sheikh Zakzaky ya umurci Sheikh Sanusi AbdulKadir da ya shirya shi a garin Kano a wannan shekaran.Yau ce rana ta uku kuma ta karshe daga cikin kwanaki uku da aka dauka ana yin taron a Markaz dake Kofar Waika Kano tarayyar Nigeriya. Bayan bude taro da addu’a da wakokin bege daga sha’irai,malamai da dama sun yi jawabai masu yawa dangane da munasabar da aka taro domin ta. Sarkin Sharifan Kano a nashi jawabin ya bayyana cewa: “Duk wanda kuka ga ya shirya taron hadin kan musulmi amma bai gayyaci ‘yan shi’a ba,munafuki ne.Ba taron hadin kai bane,taron ya za a far wa ‘yan shi’a ne da neman biyan bukatunsu kawai.Ni Bakadire ne,kuma dan darika,na yarda ‘yan shi’a musulmai ne,kuma zan yi taro da su. “Gidanmu ya kai shekara dari shida da sharifanci amma ban taba ganin tutar kabarin wani Imami ba,sai a gun ‘yan shi’a.” Sarkin Sharifan Kano ya yi kira da roko ga Sheikh Sanusi AbdulKadir cewa ‘don Allah a taimaka a shiga da wannan tuta ta Imam Ridha cikin Sharifai a zagaya mana da ita a nuna masu cewa gashi wajen ‘yan shi’a.’ Sarkin Sharifai bai karkare jawabinsa ba sai da yayi kira ga hukuma yana cewa: “Wannan taruka da ake yi na Imam Ridha sune suke zaunar da kasar nan lafiya.” Shi kuwa Sheikh Yakubu Yahaya Katsina a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a matsayin babban bako a wajen taron, yayi bayani ne game da muhimmancin riko da Imam Ali a matsayin wanda yake massala sunnar Annabi Muhummad(sawa),yana cewa: “A lokacin da aka kawo Imam Ali wajen zaben khalifa na uku an bashi zabi akan in zai yi aiki da sunnar Annabi da sunnar khalifofi guda biyu,sai Imam Ali yace;zan yi aiki da Manzon Allah.Don haka idan kana neman sunnah,to,Imam Ali shine sunnah.” Sheikh Yakubu Yahaya ya bayyana cewa ‘Sheikh Zakzaky ya riga yayi jihadi kuma ya riga ya kafu.Ya ‘yantar da zukata,sun yi bara’a kuma sun yi wilaya,an canja tunaninsu.’ Sheikh Sanusi Abdulkadir a lokacin da yake jawabinsa a matsayin mai masaukin baki,ya bayyana cewa: “Don girman Allah don matsayin Imam Ali Ar-Ridha don albarkan wannan tuta idan da wanda muka yi wa laifi,don girman wannan rana tuta ya yafe mana. “Mu idan da wanda yayi mana laifi Wallahi mun yafe masa.Ranar sa wannan tuta ta zama ranar hadin kanmu.” Taron ya samu halartan ‘yan uwa daga sassa daban daban a cikin Nigeriya a kasashen makwabta.Daga cikin wadanda suka halarci wannan taro akwai Sheikh Adamu Tsoho Jos,Sheikh Kasimu Umar Sokoto,da Malam Abubakar Nuhu Talatan Mafara da sauran manya manya wakilan ‘yan uwa almajiran Sheikh Zakzaky daga garuruwa masu yawa

  cigaba ...
 • An fara taron tunawa da munasabar haihuwan Imam Ali Ar-Rida a Kano

  Yau Alhamis,3 ga watan Agusta 2017,Harkar Musulunci a Nigeriya karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Yakubu Zakzaky ta fara gabatar da jerin tarukan da ta shirya domin tunawa da ranar haihuwan Imam Rida a Kano,wanda Ad-Da’iral Ammah ta saba shirya a duk shekara a Hussainiyyar Baqiyyatullah Zariya kafin a rusa ta. A wannan shekarar taron an fara yinsa ne a Markaz dake Kofar Waika Kano tarayya Nigeriya,kuma za a kammala taron ranar Asabar mai zuwa. Duk shekara akan canja tutar haramin Imam Ridha (as) da wata,wadda aka cire din ana kyautar da ita ga wani daga cikin masu hidima ga AhlulBait a duniya.To,a wannan shekarar an aikowa da Sheikh Zakzaky ita wannan tutan da aka cire a matsayin kyauta da karramawa.Bayan tutan ta isa ga Sheikh Zakzaky a in da yake a tsare.Sai Sheikh yayi umurni da baiwa Malam Sanusi Abdulkadir a matsayin girmamawa saboda sadaukarwansa,sannan kuma ya shirya taro na musamman dangane da Imam Ridha,sannan a sanya tutan a Hussainiyyar Markaz dake Kofar Waika. Daga cikin abubuwan da aka gudanar yau a matsayin rana ta farko daga cikin jerin kwanaki uku na taron,bayan bude taro da addu’a da karatun Alkur’ani da karatun Ziyara,an gabatar da jawabai masu muhimmanci a wajen taron. Sheikh Adamu Tsoho Jos a matsayin babban bako mai gabatar da kasida a wannan rana ya fara jawabinsa da taya ‘yan uwa murna na zagayowar wannan rana ta haihuwan Imam Ridha wanda bisa ludufin Allah ranar haihuwarsa ya zo daidai da ranar haihuwar ‘yar uwarsa Sayyidah Ma’asumah. Shehun Malamin ya bayyana cewa “dole mu godewa Allah na samun kanmu cikin masu raya al’amarin AhlulBait.Na farko,mu godewa iyayenmu da ba a same mu ba ta hanyar da ba ta dace ba,kuma mu ba munafukai bane kaman yanda ta tabbata a riwaya. “Ya zo a hadisi daga Imam Sadiq yana cewa Allah yayi rahama ga wanda ya raya al’amuran mu.Wannan irin taro namu yana daga cikin raya al’amarin AhlulBait.” Shi kuma Sheikh Sanusi AbdulKadir a na shi jawabin bayan ya godewa Allah bisa ga wannan karramawa da Sheikh Zakzaky yayi masu ba wai don ya isa bane,ya bayyana cewa: “Tutar Haramin Imam Ridha babu wadanda suke cirota sai mutum 4 a Iran,Sayyid Khamnae da wasu ne suke ciro ta.Bayan an ciro ta ana baiwa Sayyid Khamnae ya dauki tsawon lokaci yana tawassali da ita.Sannan ya dawo da ita yace a samu wani bawan Allah a duniya wanda yake yiwa addini hidima a bashi ita. “Shine sai aka aiko ta ga jagoranmu Sayyid Zakzaky.Shima ya dauki lokaci yana tawassali da ita a inda yake tsare yanzu,sannan kuma ya aiko da ita nan Kano yace a shirya gaggarumin taro.Sayyid yace ya so a ce yana nan ya shirya taron da yafi na baya amma yanzu Dr Sanusi yayi iya kokarinsa ya ga taron anyi.” Taron ya samu halartan ‘yan uwa maza da mata daga wurare daban daban cikin Nigeriya.Kuma taron yana gudana cikin nasara da taimakon Allah.

  cigaba ...
 • Ayatullah,Iran Ba Za Ta Taba Mika Wuya Ga Mulkin Kama-Karyar ba

  Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta taba kuma ba za ta taba mika kai ga mulkin kama-karya na ma'abota girman kai, yana mai cewa a halin yanzu Iran tana tsaya da kafafunta kyam sama da shekarun baya.

  cigaba ...
 • Manyan Hafsoshin mayakan Najeriya Sun Isa Birnin Maiduguri.

  Manyan hafohin mayakan Najeriya sun isa birnin Maiduguri a jihar Borno, arewa maso gabashin Nigeria biyo bayan umarnin mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbanjo cewar manyan sojojin su koma yankin da ya sha fama da hare haren yan ta’addan Boko Haram tare da yin garkuwa da mutanen yankin.

  cigaba ...
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky