• Ranar Quds ta Duniya: Anyi Muzaharan Quds a Nigeriya.

  Yau ce juma’ar karshe ta watan Ramadaan ta bana.A irin wannan ranar ce musulmi a duk fadin duniya suke fitowa domin nuna goyon bayansu ga raunanar Palasdin da raunanar duniya gabaki daya da kuma rashin amincewa da cigaba da mamayan sahayona a wannan yankin na Palasdinu. Musulmi a Nigeriya sun amsa wannan kiran na Imam Khomaini ta hanyar gudanar da Muzaharori da taruka domin nuna goyon baya ga raunanar duniya da kuma bayyana zaluncin azzulumai. Anyi irin wa’yannan muzaharori garuruwan Sokoto,Katsina,Potuskum,Kudan,Kaduna da Yola da sauran manya jihohin Nigeriya.A garin Sokoto Malam Kasimu Umar ne ya jagoranci muzahara da bayanin rufe ta.Haka nan a garin Yola Malam AbdulRahman Yola ne ya jagoranci wannan muzaharan. Kuna iya ganin wasu hotunan muzaharan a kasa

  cigaba ...
 • An Sauke Yariman Saudiyya Daga Mukaminsa

  Sarkin Saudiyyah Salman Bin Abdulaziz ya sauke yarima mai jiran gado na kasar Muhammad Bin Naif bin Abdulaziz daga kan mukaminsa na yarima mai jiran gado, tare da dora dansa Muhammad bin Salman

  cigaba ...
 • TAWAQAR ‘YAN UWA ALMAJIRAN SHEIKH IBRAHIM ZAKZAKY SUN ZIYARCI SHEIKH ABDULJABBAR SHEIKH NASIRU KABARA Da SHEHU USMAN DAHIRU BAUC

  Jiya talata,19 ga watan Yuni 2017 ne,wata tawaqa ta almajiran Sheikh Ibrahim Yakubu Zakzaky karkashin jagorancin Sheikh Yakubu Yahaya Katsina suka ziyarci Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabari a mahallin da shehin malamin yake gabatar da karatun tafsirin Alkur’anin na “Jauful Fara”. Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara malami ne masani wanda a lokaci guda kuma marubuci na kin karawa.Ya rubuta littafai masu yawa a janibobi daban daban.Sannan saboda tsabagen kauna da soyayya da shehin malamin yake nuna wa Manzon Allah da iyalan gidansa tsarkaka,ya sanya mutane daga bangaren Salafiyya suna jifan malamin Tashayyu’I. Sheikh AbdulJabbar ya amshi wannan tawaqa cikin girmamawa da farin ciki,sannan tawaqar ta nuna farin ciki dangane da irin tarbar da Sheikh yayi masu. A cigaba da ziyara ta jiya,tawaqar ‘yan uwa almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky karkashin jagorancin Sheikh Yakubu Yahaya Katsina suka ziyarci Sheikh Dahiru Usman Bauchi domin girmama da sada zumunci. Sheikh Dahiru Bauchi babban malamin addinin musulunci ne kuma yana daga cikin manya manyan muqaddiman Tijjaniyya a Nigeriya.Malami ne mahardacin kuma masanin tafsirin Alkur’ani da littafai,yana daga cikin wa’yanda karatukansu da maganarsu ke daukan hankalin jama’a a NIgeriya saboda hikima da iya bayani,ma’ana yana da tasiri matuka a cikin al’umman Nigeriya. Sheikh Yakubu Yahaya Katsina yayi taqaitaccen bayani game da dalilin wannan ziyara tasu,daga cikin abubuwan da ya fadi akwai cewa: “Dan shi’an dake zagin Sahabbai kaman dan haqiqa ne a cikin tijjaniyya ko dan izala a cikin Ahlus-Sunnah”. A lokacin da Shehu Dahiru Bauchi yake jawabin maraba ga wannan tawaqa ya shaida cewa: “Duk musulmi shi’ar Annabi Muhammadu ne,idan musulmi yace baya shi’a sai mu kore shi.Mun sha yin wazifa tare da Sheikh Zakzaky,sannan gashi kun yi sallah a bayana na kuma kun yi salatul Fatihi. “Maganar zagin Sahabbai kuwa tattaunawa da masu hankali cikinku yasa mun fahimci ‘yan haqiqan dake cikinku sune suke yi.Don haka mun yarda da abubuwanku dari bisa dari kaman yadda kuka yarda da na mu. Wannan tawaqa ta Sheikh Yakubu Yahaya tayi sallah tare da Shaikh Dahiru,sannan suka yi buda baki tare da shi a masaukinsa dake Kano.

  cigaba ...
 • AN GABATA DA ZAMAN KOTU AKAN KARAR DA SHAIKH ZAKZAKY YA SHIGAR DANGANE DA RIKE SHI BA AKAN KA’IDA BA Yau 15 ga watan Juni 2017 n

  Bayan tattaunawa da muhawara wadda ta gudana tsakanin lauyoyin Shaikh Zakzaky da lauyan soja,lauyan na soja ya nemi aba shi dama yayi nazarin karar domin wai bai fahimci abin takardun suka kunsa ba,amma Alkalin ya nuna mamakinsa ga wannan magana ta lauyan soja in da yake cewa kashi biyu cikin uku na takardun dake gabansa na sojoji ne da COAS,kuma sojoji da COAS sune manyan wadanda ake kara a takardun. Wannan ya sanya Alkalin yayi mamaki game da cewa lauyan soja bai san komai ba game da takardun da suke dauke da karar ba.Saboda haka yace ko ya bashi kwana biyu ba zai iya komai ba.Akan wannan ne lauya Falana ya nemi kotu da ta ci tarar lauyan Soja.Amma Alkali yace ba zai ci tarar lauyan ba saboda dagawar da yayi a baya na wannan shari’ar daga lauyoyin IMN ne. Daga karshe Alkalin yace zai daga wannan shari’ar don baiwa sojoji dama domin su kawo wani lauya ko kuma wannan lauyan yayi nazarin takardun sosai saboda yace bai san komai ba.Sai dai Lauya Falana ya nemi da a kai karshen maganar da lauyan gwamnati ta gabatar a baya na cewa a jira a kammala sharia’ar Abuja kafin a cigaba da wannan . Sai Alkali ya bayyana cewa yana da kwafin hukuncin Alkali Kolawale na Abuja.Ya karanta ba sau daya ba.Kolawale ya nemi da saki Sheikh Zakzaky da mai dakinsa,sannan a biya su naira miliyan 50,kuma a gina masu gida a Arewa.Amma gwamnati taki bin umurnin ne saboda wai tana basu kariya ne daga harin makwabtansa. An daga sauraron karar zuwa 30 ga wannan wata.Sannan yace dole lauyan soja yayi nazarin dukkan takardun kafin wannan ranar.

  cigaba ...
 • DALIBAI SUN YI KIRA DA A SAKI SHEIKH IBRAHIM ZAKZAKY A GARIN ABUJA NIGERIYA

  A jiya laraba ne,daliban manyan makarantu na harkar musulunci suka gudanar da muzaharar lumana a garin Abuja domin kira da gwamnatin Nigeriya da ta bi umurnin kotu ta sakin Sheikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenat wa’yanda suka kasance a tsare tun bayan lokacin da sojojin Nigeriya suka afka ma Sheikh da almajiransa a watan Disambar 2015. Shugaban kungiyar ta daliban,S I Ahmad a wata takarda da suka rabawa manema labarai wadda suka yi ma take da “Lokaci yayi da gwamnatin Nigeriya zata saki Sheikh Zakzaky” ya bayyana cewa: “Mai yasa hukumomin Nigeriya suka ki su bi umurnin babban kotu,su saki Jagoran harkan musulunci a Nigeriya,Sheikh Zakazaky tare da mai dakinsa wa’yanda suke tsare ba akan ka’ida ba? “Yanzu ta bayyana ma duniya cewa Sheikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah,suna tsare fiye da shekara daya da rabi ba tare da wata tuhuma ko laifi ba tun bayan farmakin rashin imani da sojojin Nigeriya suka kai ma malamin da almajiransa wanda yayi sanadiyyan asaran rayukan daruruwan almajiransa maza da mata da kananan yara a Zariya.Sojojin Nigeriya sun afka ma Sheikh Zakzaky da matansa a gidansa.Sun harbi malamin a wajaje masu yawa a jikinsa tare matansa,suka kashe masa ‘ya’ya a gabansa. Daliban masu muzaharan lumana din sun kasance cikin tsari sanye da riguna iri wa’yanda aka rubuta a saki Zakzaky da huluna,suna rike da banoni wa’yanda aka rubuta a saki Zakzaky da kuma gwamnati tabi umurnin kotu,suna wakoki na kira da a saki Zakzaky.An kammala muzaharan lafiya ba tare da wani matsala ba

  cigaba ...
 • Yaushe Buhari zai dawo Najeriya ?

  Likitoci da ke diba lafiyar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari sun ce a yau za su gudanar da gwaje gwaje akansa, inda sakamakon gwajin ne zai tantance lokacin da shugaban zai dawo.

  cigaba ...
 • An Kama Mutane 48 Da Ke Da Alaka Da Harin Ta'addancin Tehran

  An Kama Mutane 48 Da Ke Da Alaka Da Harin Ta'addancin Tehran A ci gaba da binciken da ake bayan harin ta'addancin Tehran wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 17, ma'aikatar tattara bayannan sirri ta Iran ta ce an cafke mutane 48 da ake zargi da hannu a jerin hare-haren na ranar Laraba data gabata.

  cigaba ...
 • Ana Gudanar Da Tarurrukan Juyayin Rasuwar Imam Khumaini (r.a) A Duk Fadin Iran

  A yau ne ake gudanar da bukukuwan juyayin rasuwar marigayi Imam Khumaini (r.a) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a duk fadin kasar ta Iran inda ake sa ran a yammacin yau Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei zai gabatar da jawabi kan hakan a hubbaren marigayi Imam din da ke wajen birnin Tehran

  cigaba ...
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky