Harin ta'addanci ya hallaka mutane 84 a Faransa

  • Lambar Labari†: 765922
  • Taska : RFI
Brief

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya bayyana kazamin harin da wani direba ya kai da mota kan masu bikin ranar Yancin kan kasar wanda ya kashe mutane 80 a matsayin harin ta’addanci.

Yayin jawabi ga al’ummar kasar shugaba Hollande ya bayyana tsawaita dokar ta bacin dake shirin karewa na watanni uku.

Shugaba Francois Hollande cikin halin kaduwa yace an kai wannan hari ne a ranar da Faransawa ke bikin ranar yancin kan su, kuma cikin wadanda harin ya ritsa da su har da kananan yara.

Hollande ya bayyana damuwa kan yadda za’ayi amfani da mota dan hallaka wadanda ke walwalar su, inda yake cewa kasar ba zata bada kai bori ya hau ba, a yaki da ta’adanci da kuma karfafa aikin da suke a Iraqi da Syria wajen yaki da ISIS.

Shugaban ya sanar da kara wa’adin dokar ta baci na watanni uku da kuma kiran sojin wucin gadi dan inganta tsaro a kasar.

Hollande yace zasu ci gaba da kai hari kan wadanda suka kawo musu hari a kasar su.

Wannan dai shine hari na uku cikin watanni 18 a kasar, kuma yana zuwa ne sa’oi kadan bayan shugaban kasar yace ba zasu tsawaita dokar ta bacin da ke shirin karewa ranar 26 ga wata ba.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky