An sa jami'an tsaron Faransa cikin shirin ko-ta-kwana

  • Lambar Labari†: 720303
  • Taska : bbc.com/hausa
Brief

Ministan cikin gidan Faransa, Bernard Cazeneuve, ya ce kasarsa ta sanya jami'an tsaro 115,000 cikin shirin ko-ta-kwana bayan harin da aka kai birnin Paris ranar Juma'a.

Mista Cazeneuve ya ce an kai karin samame a wurare 128 da ake zaton 'yan ta'adda ke buya.

Jiragen yakin Faransa sun kai sababbin hare-hare ta sama kan hedikwatar kungiyar IS da ke ikirarin kishin Musulinci ranar Litinin da daddare.

IS ta ce ita ta kai hare-hare a Paris, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 129.

Faransa tana neman Salah Abdeslam, daya daga cikin mutanen da ake zargi da hannu a kai hare-haren.

An yi amannar cewa ya tsere ta kan iyakar kasar zuwa kasarsa, Belgium.

Kerry ya yi Allawadai da hari

Shi kuwa Sakataren tsaron Amurka, John Kerry, wanda ke ziyara a Faransa, ya yi Allawadai da harin a aka kai a Paris, yana mai bayyana IS da cewa kungiyar ta masu "shan jinin" jama'a.

Mista, wanda zai gana da Shugaba Hollande, ya ce Amurka za ta hada gwiwa da Faransa domin murkushe IS.

A cewar sa, "Wannan yaki ne ba wai kawai a kan Faransa ba, an yi irinsa a Lebanon da Iraqi saboda haka yaki ne a kan manufarmu da tunaninmu, sannan kuma yaki ne a kan daukacin al'ummar duniya" 289


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky