Zanga zanga ta sa firaministan Romania yin murabus

  • Lambar Labari†: 718481
  • Taska : http://ha.rfi.fr
Brief

Firaministan kasar Romania Victor Ponta ya yi murabus daga mukaminsa bayan zanga zangar da aka gudanar sakamakon tashin gobara a wani gidan rawa da ke babban birnin Bucaharest a makon jiya, inda sama da mutane 30 suka mutu.

A wata sanarwa da ya fitar a yau laraba, Ponta ya ce, ya ajiye aikin da ya rataya a wuyarsa, lamarin da ya ke ganin zai gamsar da masu zanga zangar kan titunan kasar.

Dubban jama’a ne dai suka yi taron gangami a kan titunan birnin Bucharest a jiya talata, inda suka bukaci Ponta da ministan cikin gida na kasar da su yi murabus bayan an samu karuwar mutane da gobarar ta hallaka a gidan rawan na Colectiv .

Tuni dai aka cafke masu gudanar da gidan rawan, inda aka tuhume su da laifin kisa ba da gangan ba. 289


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky