MDD ta damu da rikice-rikice a duniya

  • Lambar Labari†: 718167
  • Taska : http://ha.rfi.fr
Brief

Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar agaji ta ICRC, sun bayyana damuwarsu kan halin da duniya ta ke ciki na tashin hankalin da ake cigaba da samu musamman yadda ya ke shafar fararen hula.

Bangarorin biyu sun bukaci daukar matakan kawo karshen azabar da talakawa ke fuskanta saboda rashin tsaro.

Wata wasikar hadin guiwa da shugabanin biyu Ban Ki Moon da Peter maurer suka rabawa manema labarai, sun bukaci gwamnatocin duniya da su kara kaimi wajen ganin sun samo bakin zaren warware rikice rikicen da ake fama da su yanzu haka.

Shugabannin sun kuma bukaci shugabannin su hada kan su wajen samo dabarun sasanta rikice rikice da kuma mutunta dokokin kasa, da gudanar da bincike mai inganci kan karya dokokin duniya domin hukunta masu laifi da kuma tabbatar da cewar an yi amfani da doka.

Ban ki-Moon da Peter Maurer sun kuma yi allawadai da wadanda ke karya dokokin duniya, musamman wajen kai hari kan fararen hula da gine ginensu.

Shugabannin sun kuma bukaci bai wa jami’an aikin agaji damar isa inda aka samu tashin hankali ko haddura don kai dauki ba tare da matsala ba da kuma kaucewa amfani da muggan makamai kan fararen hula. 289


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky