Jamusawa na zargin Merkel da cin amanar kasa

  • Lambar Labari†: 717695
  • Taska : http://ha.rfi.fr
Brief

Masu gabatar da kara a Jamus sun karbi koken jamusawa kimanin 400 da ke zargin shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel da cin amanar kasa kan batun karbar ‘yan gudun hijira.

Bangaren masu ra’ayin rikau ne a kasar jamus ke tuhumar Angela Merkel da cin amanar kasa kan tsarin gwamnatinta na bude kofa ga bakin ‘yan gudun hijira.

Masu gabatar da kara a Jamus sun ce sun karbi koken mutane Kimanin mutane 400 da ke zargin shugabar gwamnatin kasar.

Kuma koken da mutanen suka shigar dukkaninsu suna da nasaba ne da adawa da matakan Angela Merkel na karbar ‘yan gudun hijira

Sai dai ana ganin koken na ‘yan adawa akan Merkel ba zai yi wani tasiri ba saboda akwai abinda doka ta tanadar kafin a zargi mutum da laifin cin amanar kasa.

A bana dai Jamus ta yi alkawalin karbar bakin ‘Yan gudun hijira kimanin miliyan 1 da ke gujewa yaki a kasashen Syria da Iraqi wadanda ke ci gaba da kwarara zuwa kasashen Turai. 289


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky