An kashe Sojin Ukraine 7 a fada da 'yan tawaye

  • Lambar Labari†: 648288
  • Taska : http://www.hausa.rfi.fr/
Brief

Akalla Sojin kasar Ukraine 7 ne aka kashe a wani dauki-ba-dadin da aka yi, tsakanin sojin gwamnatin da ‘yan tawaye masu goyon bayan kasar Rasha a yankin gabashin kasar ta Ukraine

Dakarun gwamnatin kasar ta Ukraine sun bayyana a wata sanarwa da suka gabatar cewar wannan ne mafi munin kisan da aka gani makwanni 3 da suka gabatar, inda suka bayyana cewar baya ga wadanda suka mutu, akwai kuma wasu mutane 7 da suka jikkata.

Rundunar Sojin kasar ta Ukraine ta bayyana cewar ‘yan tawayen sun fi karfin jajircewa ne a yankin kudancin kasar Ukraine na Donetsk, inda har yanzu gwambatin kasar Ukraine din ke kulawa da shi.

Majalisar dunkin Duniya dai ta yi kiyasin cewar ya zuwa yau, akalla fadan da ake tsakanin Sojin Gwamnati da ‘yan tawayen, ya yi sanadin mutuwar akalla mutane Dubu  3 da 700, wadanda akasarinsu fararen Hula ne.

Wani harin da aka kai ta sama kuma ya yi sanadin mutuwar wasu ‘yan tawaye masu yawa a yankunan Gorlivka da Donetsk Garuruwan da gwamnati ke kulawa da su, a yayin da aka jikkata wasu mutanen. ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky