An yi arangama tsakanin yan sanda da masu hankoron kishin kasa a Ukraine

  • Lambar Labari†: 644575
  • Taska : http://www.hausa.rfi.fr/
Brief

An yi arangama a jiya talata tsakanin ‘yan kishin kasa da kuma ‘yan sandar kasar Ukraine a harabar ginin majalisar dokokin kasar da ke tabbatar da sabon ministan tsaron kasar a kan mukaminsa.

Masu tarzomar dai sun jefa bakin wuta a cikin ginin majalisar, da kuma karya wasu muhimman kadarori na majalisar, abinda shugaban kasar Petro Poroshonko ya bayyana shi da cewa zagon kasa ne.

Kasar Ukraine dai bata bukatar irin wadannan tashe tashen hankulla, ganin yadda a halin yanzu dakarunta ke tabka fada a yankin gabashi, da yan aware masu goyon bayan Rasha

Kasashen turai dai na ci gaba da kakabawa kasar Rasha, tankunkuman kariyar tattalin arziki da nufin tilasta mata tsame kanta daga goyawa yan awaren na Ukraine da suke zargin da yi, da kuma cewa ita ce, ta kirkirosu domin cimma muradunta na kokarin fadada kasarta. ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky