Yau ake zaben raba-gardama a yankin Scotland na Ingila

  • Lambar Labari†: 638635
  • Taska : http://www.hausa.rfi.fr/
Brief

A yau Alhamis mazauna yankin Scotland na gudanar da zaben raba-gardama dangane da samun ‘yancin kai daga kasar Birtaniya

A cikin Daren jiya ne dai aka kammala yakin neman zabe tsakanin masu goyon bayan da kuma masu adawa da ‘yancin-kai.

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a da wasu cibiyoyi masu zaman kansu suka shirya, na nuni da cewa har zuwa yammacin jiya wadanda ke adawa da batun ballewar ne suka fi samun karbuwa da kimanin kashi 52 cikin dari, to sai dai duk da haka manazarta na kallon zaben na yau a matsayin wanda zai iya zuwa da sakamako na ba zata.

Shugaban gwamnatin yankin na Scotland Alex Salmon daya daga cikin masu ra’ayin ballewar, ya bayyana cewa samun ‘yancin-kai daga Birtaniya shi ne abin da ya kamata mazauna yankin Scotland sun amince da shi a yau.

To sai dai tsohon Firaministan Birtaniya Gordon Brown, jagora a gungun masu adawa da samun ‘yancin, ya bayyana wa taron magoya bayansa a birnin Glasgow cewa, ci gaba da kasancewa hade da Birtaniya, shi ne zai bai wa mazauna yankin Scotland damar fada a ji a duk wasu batutuwa da suka shafi kasar.

Yau dai shekaru 307 kenan da yankin na Scoltand ya amince da kasancewa a cikin Birtaniya, kuma kuri’ar ta yau ce za ta fayyace makomar wannan kawance. ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky