Kungiyar NATO Zata Kara Karfinta A Gabacin Turai Saboda Rikicin Ukrain

  • Lambar Labari†: 635149
  • Taska : http://hausa.irib.ir/
Brief

Shugaban kungiyar tsaro ta NATO General Anders Fogh Rasmussen ya bayyana a jiya litinin
cewa gwamnatin kasar Rasha tana da hannu dumu dumu a cikin rikicin da ke faruwa a gabancin kasar Ukrai don haka kungiyar NATO zata kara karfin samuwarta a gabancin Turai don fuskantar barazanar ta Rasha.

Babban sakatarin kungiyar tsaron ya bayyana haka ne a jiya litinin, ya kuma kara da cewa shuwagabannin kungiyar zato gudanar da taron gaggawa a karshen wannan makon don tattauna kan matakin da yakamata su dauka kan kasar Rasha da kuma yadda zasu tallafawa Ukrain.

A birnin London kuma Primistan kasar Britania Devide Cameron ya fadawa majalisar dokokin kasar cewa sojojin Rasha suna fada da sojojin kasar Ukrain kafada da kafada da yan tawayen kasar. Wanda hakan inji shi ya sabawa yencin mutanen kasar.

A jiya ne dai aka fara wani taron tattaunawa tsakanin wakilan Rasha, da na gwamnatin kasar Ukrai da kuma na yan tawayen a birnin Minsk na kasar Belerus.

Shugaban kungiyar tsaro ta NATO General Anders Fogh Rasmussen ya bayyana a jiya litinin cewa gwamnatin kasar Rasha tana da hannu dumu dumu a cikin rikicin da ke faruwa a gabancin kasar Ukrai don haka kungiyar NATO zata kara karfin samuwarta a gabancin Turai don fuskantar barazanar ta Rasha.

Babban sakatarin kungiyar tsaron ya bayyana haka ne a jiya litinin, ya kuma kara da cewa shuwagabannin kungiyar zato gudanar da taron gaggawa a karshen wannan makon don tattauna kan matakin da yakamata su dauka kan kasar Rasha da kuma yadda zasu tallafawa Ukrain.

A birnin London kuma Primistan kasar Britania Devide Cameron ya fadawa majalisar dokokin kasar cewa sojojin Rasha suna fada da sojojin kasar Ukrain kafada da kafada da yan tawayen kasar. Wanda hakan inji shi ya sabawa yencin mutanen kasar.

A jiya ne dai aka fara wani taron tattaunawa tsakanin wakilan Rasha, da na gwamnatin kasar Ukrai da kuma na yan tawayen a birnin Minsk na kasar Belerus.

Shugaban yan tawaye na kasar ta Ukrain Andrei Purgin ya ce zasu yi amfani da taron na Minsk wajen shelanta samun yencin yankin gabacin kasar ta Ukrai daga kasar. ABNA

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky