Kungiyar Tarayyar Turai EU Tayi Barazanar Kakabawa Kasar Rasha Takunkumi

  • Lambar Labari†: 634725
  • Taska : http://hausa.irib.ir/
Brief

Kungiyar Tarayyar Turai ta baiwa kasar Rasha maku guda na kawo karshen shiga bayan 'yan aware a gabacin kasar Ukreine.

  Kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa ya habarta cewa bayan wani taron gaggawa da ta kira a birnin Brussels kungiyar EU ta baiwa kasar Rasha wa'adin  maku guda na kawo karshen goyon bayan 'yan aware na gabacin kasar Ukreine a yakin da suke yi da Gwamnatin Ukreniya idan kuma ba haka ba kungiyar da EU ta ce za ta sake kakabawa kasar ta Rasha sabon takunkumi karya tattalin arziki.   A yau lahadi  shugaban hukumar tarayyar Turai José Manuel Barroso,ya ce wajibi ne su baiwa kasashen dake cikin wannan kungiyar dama na  tsahon maku guda domin su tanadi kayayyaki da suke bukata daga kasar Rasha kafin kakaba takunkumin.   Mazu nazari kan harakokin siyasa na ganin cewa kungiyar ta EU tana  sara tana dubin bakin katari , saboda irin illar da wannan takunkumi zai janyowa kasashen na Turai. Kasar Rasha dai itace kasa ta uku mai karfin masana'antu a kungiyar tarayyar turai kuma daya daga cikin kasashen dake wadatar da kungiyar da men fetur gami da iskar gaz.       ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky