Mai yuwa ne a gana a karon farko tsakanin Rasha da Ukraine

  • Lambar Labari†: 633598
  • Taska : http://www.hausa.rfi.fr/
Brief

Ana shirin ganawa karon farko tsakanin gwamnatin kasar Ukraine da ta Rasha dangane da batun samar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu da ya tabarbare sakamakon fadan da 'yan tawayen Ukraine masu goyon bayan Rasha ke yi da Dakarun kasar tasu

Yau Talata 26 ga watan Agusta ne ake sa ran shugaban kasar Russia, Vladimir Putin a karon farko zai gana da shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko a cigaba da lalabo hanyar magance rikicin kasar Ukraine a yakin da take da ‘yan tawaye masu samun goyon bayan kasar Rasha.

Rikicin kasar Ukraine din dai na kara zafafa ne a yayin da kasar ta Ukraine ta yi ikrarin cewar Dakarunta sun fafata da wata Runduna da ta tsallako kan iyakar kasar, inda kuma take kyautata zaton cewar Dakarun kasar Rashan ne.

Wannan ikrarin na kasar Ukraine kuma ya tada tsimin kasar Rasha inda hukumomin kasar suka bayyana hakan a matsayin labarin da babu kamshin gaskiya a ciki, harma tana cewar muddin wannan labarin ya tabbata ba gaskiya ba, to abinda zai biyo baya ba dadi zai yi ba.

Koda yake wani jagoran ‘yan tawayen kasar Ukraine masu goyon bayan kasar Rashar ya fada cewar sun dan kara da wasu mayaka a yankin gabashin kasar da ‘yan tawaye ke ci gaba da rikewa.

Kasar Amurka dai ta sake gargadin Rasha kan kutsen da ta ce jami’an ta na yi zuwa cikin kasar Ukraine bayan gwamnatin kasar ta ce ta kama wasu ‘yan kasar Rasha 10 a cikin kasar.

Mai baiwa shugaban kasar Amurka shawara kan harkokin tsaro, Susan Rice ta bayyana kutsen a matsayin takalar da ba zasu amince da it aba.

Dama dai kasashen Turai da Amurka na hararan kasar Rasha akan batun rikicin kasar Ukraine da suka ce it ace take gidada shi.

Rasha dai ta sha musanta hakan amma kasashen Turai na kayatawa, harma sun dauki matakan kakabawa Rasha Takunkumman karya tattalin arziki da manufar karya lagon kasar ta Rasha, amma Rasha ta bayyanawa Duniya cewar ko a jikinta, kuma kasar Amurka da kanta ce za ta bukaci a cire Takunkumman dan ta fara dandana kudarta. ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky