A Afghanistan An Kashe Shugaban Khorasa Kungiyar Dake da Alaka da ISIS

  • Lambar Labari†: 810742
  • Taska : VOA
Brief

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe Wani babban kwamandan kungiyar Khorasa, wadda reshen kungiyar ISIS ce, wadda kuma aka ce tana da hannu dumu-dumnu a cikin jerin hare haren kunar bakin wake da wasu munanan ayyuka.

An dai kashe wannan dan talikin ne a wani martanin harin ta’adanci da aka kai a gabashin Afghanistan, kamar yadda jami’an Amurka da na Afghanistan din suka ruwaito jiya Alhamis.

Shi dai wannan kwamanda mai suna Qari Munib, an kashe shi a sailin wata arangama da a kayi wanda dakarun Afghanistan da taimakon sojojin Amurka suka kai a gabashin Afghanistan da niyyar murkushe ayyukan ta’addanci a yankin.

Kamar yadda sanarwar da ta fito daga ma’aikatar tsaron Amurka ta Petagon ke cewa a jiya Alhamis, wannanharin ya faru ne a ranar tara ga wannan watan a gundumar Achin dake lardin Nangarhar.

Sanarwar da Pentagon ta fitar da ofishin shugaba Asharaf Ghani, shugaban Afghanista, sun bayyana cewa Munib shine kanwa uwar gami na tagwayen hare-haren da aka kai a Kabul da dai wasu ayyukan assha da aka gudanar a gundumar Achin na lardin Naganhar wanda ke bakin iyaka da kasar Pakistan.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky