Syria Ta Yi Watsi Da Rahoton Amnesty

  • Lambar Labari†: 810295
  • Taska : Pars Today
Brief

Gwamantin Syria ta yi watsi da rahoton kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa wato Amnesty International mai cewa an kashe dubban mutane a Kurkukun kasar a asirce.

Ma'aikatar shari'a ta Syria ta ce ko kadan babu kamshin gaskia a wannan rahoto wanda na cin fuska ne ga kasar ta Syria a idon duniya.

Rahoton wanda Amnesty ta fitar ya ce an kashe kimanin mutum dubu 13 a asirce a gidan yarin na Saydaya dake kusa da birnin Damascos.

Rahoton ya kuma ce mafi yawan mutanen da ake kashewa fararen hula ne wanda ake kashewa ta hanyar rataya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky