Hare-Haren Ta'addancin H.K.Isra'ila Kan Palasdinawa Suna Ci Gaba Da Janyo Bullar Cututtuka

  • Lambar Labari†: 807770
  • Taska : Pars Today
Brief

Majiyar lafiya a yankin Zirin Gaza na Palasdinu ta sanar da cewa: Hare-haren wuce gona da irin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar Palasdinu musamman yankin Zirin Gaza suna ci gaba da janyo bullar muggan cututtuka.

Shugaban bangaren kula da cututtukan kunne a cibiyar kula da lafiyar yara a yankin Zirin Gaza na Palasdinu Ramadhan Husain ya bayyana cewa: Fashe-fashen manyan makamai musamman bama-bamai da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suke harbawa kan yankunan Palasdinawa da suke Zirin Gaza, suna mummunan tasiri a kafar jin kananan yara lamarin da ke kai wasu daga cikin yaran ga kurmancewa. 

Har ila yau Raja'e Sharaf shugaban bangaren kula da cutar kunne a asibitin Hammad da ke yankin Zirin Gaza ya bayyana cewa: Ana cigaba da samun bullar matsalolin rashin ji sosai ko kurmantaka sakamakon hare-haren wuce gona da irin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila suke kai wa kan gidajen Palasdinawa, inda daga shekara ta 2014 zuwa yanzu akwai kananan yara 38,000 da suke fama da matsalolin ji a yankin na Zirin Gaza.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky