Wani Bom Da Ya Fashe Ya Kashe Mutane Da Dama A Syria

  • Lambar Labari†: 803018
  • Taska : Pars Today
Brief

Wata mota makare da boma bomai ta tarwatse a garin Jablah a lardin Lantakia daga yammacin kasar Syria a yau Alhamis, kuma ta yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 15 da kuma raunata wasu kimani 35.

Tashar television ta Presstv a nan Tehran ta ce babu wanda ya dauki alhakin tada boma boman amma hakan ya faru ne a dai dai lokacinda ake tsagaita bude wuta tsakani sojojin gwamnatin kasar Syria da kawayenta da kuma yan ta'adda wadanda suke samun tallafin kasashen waje. 

Kamfanin dillancin labaran SANA na gwamnatin kasar Syria ya bayyana cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu ya kai 11, sai dai jami'an gwamnatin kasar Rasha da kuma syria sun bayyana cewa tun bayan tsagaita bude wuta tsakanin bangarorin biyu an sha samun keta hurumin yerjejeniyar tsagaita bude wutan a wurare daban daban daga bangaren yan ta'adda.

Yankin Jablah da Kuma Tartus dai basu cika fuskanta irin wadan nan hare hare kamar na yau Alhamis ba tun lokacinda aka fara rikicin kasar ta Syria shekaru 5 da suka gabata.

Wasu bayanai sun bayyana cewa a cikin watan mayun shekarara da ta gabata ne kadai yan ta'adda suka taba kai hari a wadan nan wurare.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky