Wata Kotu A Kasar Jordan Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Yan Kungiyar Daesh Biyar

  • Lambar Labari†: 801346
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Wata kotu a kasar Jordan ta yanke hukuncin kisa kan mutane biyar wadanda suka kasance yan kungiyar Deash, sannan ta yanke hukuncin dauri ga wasu 15.

Tashar television ta Presstv a nan Tehran ta bayyana kotun ta yanke hukuncin a kan wadan nan yan ta'adda 20 ne a yau Laraba, kuma ta kara da cewa ta kama mutanen da laifin kashe jami'in tsaro guda, mallakar makamai, harhara boma bomai da kuma samunsu da mummunanr ikida mai kafirta mutane ne.

Labarin ya kara da cewa a cikin watan Maris na wannan shekara mai karewa ne jami'an tsaron kasar ta Jordan suka kai sumame wajen mabuyar yan ta'addan a garin Irbid a tsakiyar kasar, sannan bayan musayar wuta jami'an tsaro suka sami nasarar kashe 7 daga cikinsu sannan suka kama wasu 20.. Sai jami'an tsaron sun rasa dansanda guda a farmakin. Za'a aiwatar da kisan mutanen guda 5 ne ta hanyar ratayewa, a yayinda wadanda ake dauke kuma zasu yi aiki mai wahala a gidajen yarin da zasu zauna. 

Kasar Jordan dai tana daga cikin kasashe 40 kawayen Amurka masu riya yaki da kungiyar ta Daesh a kasashen yankin, sai dai mutanen kasar da dama sunan ganin kawancin ba abnda zai jawowa kasar sai karin tashe tashen hankula, da kuma kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky