A Cikin Shekara Daya Yan Ta'adda A Kasar Iraqi Sun Kashe Mutane 12,000

  • Lambar Labari†: 800938
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa mutanen kasar Iraqi kimani dubu 12 ne suka rasa rayukansu a hannun yan ta'adda a cikin shekara ta 2016 mai karewa.

Tashar Television ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa kamfanin dillancin labarai na Anadolu news na gwamnatin kasar Turkia ne yake bawa majalisar  rahoton wata wata kan yawan mutanen da yan ta'adda suka kashe a kasar ta Iraki a duk tsawon shekarar.

Labarin ya kara da cewa mutane 12,038 aka kashe a yayinda wasu 14,411 kuma suka ji rauni tun farkon shekara ta 2016. Banda haka labarin ya kara da cewa fararen hula 6,492 aka kashe a cikin wannan adadin, sannan jami'an tsaro kuma 5,546.

Har'ila yau kamfanin dillancin labaran na Anadolu ya sami na shi rahoton ne daga jami'an kiwon lafiya da kuma jami'an tsaron kasar ta Iraqi da suke  yankunan Bagdaza, Salahuddeen, Ninawa, Kirkuk, Ambar da kuma Diyala. 

Wadan nan mutane dai sun rasa rayukansu ne ta hanyoyi daban daban wadanda suka hada da  harbe harbe da bindiga, tada boma bomai a cikin motoci da gine gine, harin kunan bakin wake da kuma fafatawa da mayakan kungiyoyin yan ta'adda a yankuna daban daban na kasar.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky