Wasu 'Yan Ta'adda 'Yan Asalin Kasar Tunisiya Daga Kasashen Syria Da Iraki Sun Koma Kasar su

  • Lambar Labari†: 800509
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Daruruwan yan ta'adda masu tsatsauran ra'ayin addinin sun koma gida Tunisia daga kasashen Iraqi Siriya da kuma Libya

Ministan harkokin cikin gida na kasar ta Tunisia Haadee Majdub ne ya bayyana haka a yau Asabar.ya kuma kara da cewa sun sami labarin cewa yan ta'adda yan asalin kasar ta Tunisia kimani 800 suka dawo kasar daga ayyukan ta'addanci da suka yi a kasashen Libya, Iraqi da Siriya. Majdub ya ce hukumar yan sandan ci na kasar basu yi aikinsu da ya dace ba a wannan bangaren, amma a halin yanzu ya bada umurnin su tabbatar da cewa sun gano wadan nan mutane don a rika sanya ido a kan ayyukansu.

Labarin ya kara da ce mafi yawan yan kungiyar Daesh wadanda suka aikata ayyukan ta'addanci a wadan nan kasashen Larabawa daga kasar ta Tunisia ne suka foto.

Sannan a shekara ta 2015 yan ta'addan a cikin gida sun kashe jami'an tsaron kasar 53 sun kuma kai hare hare kan baki masu yawon bude ido suka kashe da dama daga cikinsu, wanda haka ya lalata kafar yawon shakatawa wacce gwamnatin kaar take samun kudaden shiga ta bangaren.  288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky