Tashar television ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Turkia Mevlut Cavusoglu yana fadar haka a wani taron da kasashen da suke goyon bayan yan ta'adda a kasar Siria suke gudanarwa a birnin Jadda na kasar Saudia.
Ministan yana fadar haka ne bayan da sojojin siria da kawayenta suka fatattaki yan ta'adda daga birnin Halab na kasar ta Siria a ranar Alhamis da ta gabata, sannan sun sha alkawarin cewa zasu ci gaba da fatattakan yan ta'addan a sauran yankunan kasar Siria da suke rika ta har zuwa kubutar da dukkan yankunan kasar daga hannun yan ta'adda.
Kasashe masu goyon yan ta'adda a yankin, wadanda suka hada ita Turkia, saudia da kuma wasu kasashen yankin suna gudanar da taron gaggawa a kasar Saudai tun tattauna matakan da zasu dauka bayan sha kaye a kokarinsu na sauke shugaba kasar Siria Bashar al-asad da karbin bingida.288