Gwamnatin Syria ta yabawa Rasha bisa karbo Aleppo

  • Lambar Labari†: 800156
  • Taska : RFI
Brief

Shugaban kasar Syria Bashar al Assad ya yabawa kasashen Rasha da Iran kan gagarumar rawar da suka bayar, wajen kakkabe ‘yan tawayen kasar daga birnin Aleppo.

Assad yace ‘yantar da Aleppo ba nasara ce ga Syria kawai ba, nasara ce ga daukacin masu yaki da ta’addanci, musamman kasashen Rasha da Iran.

Kungiyar agaji ta Red Cross tace akalla ‘yan tawaye 4,000 ne suka fice daga gabashin Aleppo, yayinda ake ci gaba da kwashe fararen hula daga yankin.

Tun a shekara ta 2012 irnin Aleppo ya kasu gida biyu wato bangaren da sojojin gwanati ke iko da shi, da kuma yankin da ‘yan tawayen suka mamaye.
Majalisar Dinkin Duniya tace yanzu haka masu sa ido 31 ke Aleppo domin ganewa idonsu yadda aikin kwashe fararen hular ke gudana.

Karbe gabashin Aleppo gagarumin koma baya ne ga yunkurin mayakan ‘yan tawaye Syria na kifar da gwamnatin kasar, wadanda suka kaddamar da fafutukarsu a shekara ta 2011.

ama da mutane 300,000 suka rasa rayukansu tun bayan barkewar yaki a Syria.288

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky