Sabon Kakakin ISIS Ya Kira 'Yan Kungiyar Su Farma Makiyansu Koina A Duniya

  • Lambar Labari†: 796395
  • Taska : VOA
Brief

Sabon kakakin kungiyar ISIS da aka nada yana kira akan magoya bayan kungiyar a ko ina suke a duniya da cewa su tasarwa makiyan kungiyar, suyi ta fattakarsu har, kamar yadda yace, sai “sun kona wutar dake karkashin kafafunsu.

A cikin wani faifan da sashenta watsa labarai na al-Furqan ya sako ne, ISIS ta bada sanarwar nada Abu hassan al-Muhajir sabon kakakinta don ya maye gurbin Abu Muhammad al-Adnani wanda wani harin Amurka ya hallaka shi a kusa da garin al-Bab na kasar Syria a cikin watan Agustar da ya wuce.

A cikin faifan ne aka ji al-Muhajir yan kira ga magoya bayansu da cewa su kadarwa makiyan nasu a ko ina suka same su, kama da kasuwanni, kan hanya, a cikin gidajen holewa da ma duk sauran wurare.

Haka kuma, a cikin jawabin da ya wa lakabi “Zaku tuna abinda na gaya muku”, al-Muhajir yayi alkawarin cewa kungiyar tasu zata kai sababbin hare-hare akan kasashen Amurka, Rasha, Tura,i Iran da kuma Turkiyya, wacce daga cikin dukkan kasashen, itace ya fi caccaka sosai.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky