Amurka ta gargadi Pakistan game da kungiyar Save the Children

  • Lambar Labari†: 695212
  • Taska : rfi
Brief

Amurka ta gargadi Pakistan kan illolin da korar kungiyar agaji ta Save the Children, daga kasar da hukumomin birnin Islamabad suka yi.
Hukumomin na birnin Washington sun bayyana damuwa kan matakin da kasar ta dauka, inda suka ce zai yiwa kasar illa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin na Pakistan suka yi barazanar sake koran wasu kungiyouyin agajin kasashen waje daga kasar.
Dama hukumomin kasar Pakistan sun alakanta kungiyar ta Save the Children, mai shalkwata a akasar Britaniya, da wani likitan kasar mai suna Shakeel Afridi, da aka ce kungiyar leken asirin Amurka ta CIA.
Hukumomin na Islamabad sunce CIA tayi amfani da Likita Shakeel Afridi cikin shekarar 2012, ta hanyar aikin riga kafin boge, don gano inda shugaban kungiyar Al-Qaeda Osama bin Laden ke boye, inda aka kashe shi a wani gida dake birnin Islamabad.228


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky