• Yan Shi’a Mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky Sun Yi Taro Domin Wafatin Manzon Allah (sawa) A Fadin Tarayyar Nijeriya

  Jiya Juma’a tayi daddai da 27 ga watan Safar a lissafin wata a Nijeriya wadda a irin wannan ranar ce Manzon Allah (SAAw) ya bar duniya zuwa ga Allah Subhanahu wa Ta’ala. Sananne tsakanin musulmi ‘yan shi’a a duk inda suke suna zama suna raya wannan rana da addu’o’I da ziyarori da karanta siran Annabi (saw) domin daukan darasi. Mabiya Sheikh Zakzaky Kaman sauran ‘yan uwansu ‘yan shi’a na duniya sun gabatar da wannan taro a wurare da dama a fadin tarayyar Nijeriya. Sheikh Adamu Tsoho Jos a lokacin da yake bayani a wajen taron garin Jos ya tattauna abubuwa masu yawa dangane da wasicin Annabi (saw), yayi bayanin abubuwan da suka faru a Hajjin bankwana da yanda Annabi ya kalifantar da Imam Ali a Ghadeer. Shehin Malamin ya tabo batun rundunar Usama wadda Manzon Allah ya kawwana ya sanya Usama ya jagoranci Sahabbai zuwa Yemen, da rashin bin Umurnin Manzon Allah na fita tare da Usama zuwa Yemen da Sahabbai suka yi. Malamin yayi bayani dangane da rashin lafiyar Annabi a karshen rayuwarsa da abubuwan da suka faru a Raziyatu Yaumil khamis inda Sahabbai suka saba umurnin Manzon Allah na bashi tawada da abin rubutu a lokacin da ya bugace su da su bashi takarda da abin rubutu domin ya rubuta masu abinda idan suka rike shi ba zasu halaka ba har abada. Shi kuma Sheikh Sanusi Abdulkadir a lokacin da yake gabatar da jawabin a taron tunawa da wafatin Annabi a garin Kano yayi bayyana cewa wannan rana ce da bakin ciki da jajantawa ‘yan uwa musulmi. Sannan yayi bayani dangane da muhimmancin rubuta wasiya inda yake cewa a mazhaban Ahlulbait wajibi ne yin wasiya, ko a fadawa amintattu ko a rubuta a ajiye, amma rubutawa ya fi muhimmanci. Malamin ya bayyana cewa wasiyyar Manzon Allah ta kasu kashi kashi ne; Akwai wadda Manzon Allah yayi a ranar Arfa, da wadda yayi a ranar Gadeer, da kuma wadda yayi a lokacin da ya kwanta rashin lafiyar ajali. Idan a koma jawabin malamin za a ji yanda yayi bayani dalla dalla dangane da wadannan wasiyoyi na Annabi kafin ya bar duniya a 27 ga Safar. Sheikh Yakubu Yahaya ya bayyana cewa sau biyu ana ba Annabi guba a lokacin da yake jawabi a wajen taron tunawa da ranar wafatin Manzon Allah a Markazin almajiran Sheikh Zakzaky dake Katsina. Yana cewa “ An ba Annabi guba har sau biyu; Na farko, wata mata Bayahudiyya ta bashi guba cikin cinyar Akuya. Na biyu kuma, wasu mutane har da manyan Sahabbai ne suka sanya ma Annabi guba a cikin magani, sun bashi yace su sha ya gani, duk da haka sai da suka sanya mashi har ta zama sanadiyyar wafatin Annabi (saw)” Ayi irin wannan taro a garuruwan da suka hada Zariya, Bauci, Sokoto, Kauran Namoda da sauransu cigaba ...

 • Zimbabwe : Mugabe Ya Fito Bainar Jama'a

  A Karon farko tun bayan da sojoji suka kwace iko da wasu mahimman wurare a Harare babban birnin kasar Zimbabwe, shugaban kasar Rober Mugabe ya fito fili bainar jama'a cigaba ...

 • Mutane 18 sun mutu a harin Maiduguri

  Akalla mutane 18 sun rasa rayukansu yayin da 29 suka jikkata sakamakon wani hari da ‘yan kunar bakin wake suka kaddamar a yamamacin jiya a birnin Maiduguri da ke jihar Borno ta Najeriya. cigaba ...

 • Matsin Lambar Bayan Fage Na Fitar Iran Daga Siriya

  Duk da cewa kasar Iran, kasa ce da ta tsayin daka wajen fada da kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar Siriya, to sai dai a yayin da ake gaf da kawo karshen 'yan ta'addar, masu goyon bayan su na kokarin fitar da kasar Iran din ta bayan fage daga kasar Siriya, domin share fage na sake dawo da 'yan ta'addar a yankin. cigaba ...

 • Tarayyar Turai Bazata Dorawa Iran Takunkumi Ba

  Kwamishinan ayyukan noma da kuma raya karkara na tarayyar Turai Mr Phil Hogan ya bayyana cewa ba wata kasa a cikin tarayyar turai da take da tunanin dorawa Iran takunkumi idan Amurka ta yi watsi da yerjejeniyar da ta kulla da ita. cigaba ...

 • Saudiyya Ita Ce Tushen Tsaurin Ra'ayi Da Ta'addanci

  Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar Iran, Bahram Qassemi, kasar Saudiyya ita ce tushe kana kuma mahaifar tsaurin ra'ayi da ayyukan ta'addanci, sannan kuma babbar alama ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidajen kasashen yankin Gabas ta tsakiya. cigaba ...

 • 'Yan Shia Mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky Sunyi Taron Arba'in A Abuja

  Yau Juma'a 10 ga watan Nawumba, 'yan Shia mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky suka yi taron Arba'in na shahadar Abu Abdillahil Husain da zanga zangar neman gwamnati da ta gaggauta sakin jagoransu Sheikh Zakzaky wanda ya kusa cika shekaru biyu a tsare duk da umurnin kotu da a sake shi. 'Yan Sanda sun yi kokarin tarwatsa masu zanga zangar ta hanyar harba ma masu zanga zangar barkonon tsohuwa amma duk da haka sai da suka isa in da suke so su isa da zanga zangar. Ya zuwa hada wannan labari babu rasa rayuka amma akwai wa'yanda suka samu rauni. An rufe zanga zangar ne a farfajiyar Fountain dake Abuja. cigaba ...

 • Miliyoyin Masoya Ahlulbaiti Na Gudanar Da Tarukan Juyayin Arba'in A Karbala

  Rahotanni daga kasar Iraki na nuni da cewa miliyoyin mabiya da masoya Ahlulbaiti (a.s) daga duk fadin duniya suna ci gaba da taruwa a birnin Karbala na kasar Irakin don gudanar da juyayin Arba'in na Imam Husain (a.s) don tunawa da cikar kwanaki 40 da kisan gillan da aka yi wa Imam Husainin da iyalai da magoya bayansa a shekara ta 61 bayan hijirar Ma'aiki (s). cigaba ...