Amurka : Dan Bindiga Ya Hallaka Mutane 50 A Orlando

  • Lambar Labari†: 759782
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Rahotanni daga Amurka na cewa mutane 50 ne suka hallaka a yayin da wwani dan bindiga ya bude wuta kan jama'a a wata mashaya da masu auren jinsi daya ke taruwa a birnin Florida na Orlando.

'Yan sandan Orlando sun bayyana cewa tuni dan bindigar da ya bude wutar a wani gidan rawa na Pulse da ke tsakiyar birnin ya mutu a musayar wuta da 'yan sanda, kuma a cewar tashoshin talabijin na CBS da NBC tuni aka tantance mitimin da sunan Omar Mateen dan Amurka aman dan asalin kasar Afganistan.

ko baya ga wadanda suka hallaka a musayar wutar an samu mutane 53 da suka jikkata kamar yadda maganin birnin Buddy Dyer ya sanar.

kawo yanzu dai hukumomin yankin sun ce babu wata barazana, aman saboda yadda hankula jama'a suka tashi, magajin birnin ya bukaci gwanan na Florida daya ayyana dokar ta baci.

tuni dai hukumar FBI ta budda bincike kan ayyukan ta'adanci domin sanin mutimin ya aikata hakan ne kashin kan sa ko kuma ya samu umurni daga wajen kasar.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky