Baraka a jam'iyyar dan takara Donald Trump

  • Lambar Labari†: 752377
  • Taska : RFI
Brief

Bisa dukkan alamu Baraka a Jam’iyyar Republican na dada fitowa fili sakamakon baiwa Donald Trump tikitin takarar zaben shugaban kasar.

Wasu daga cikin kusoshin jam'iyyar ta Republican a Amurka sun bayyana damuwa dangane da zabin Donald Trump a matsayin dan takarar jam'iyyar.

Tsoffin shugabanin kasar biyu George Bush da mahaifin sa da kuma shugaban Majalisar wakilai Ryan paul sun bayyana cewar ba zasu goyi bayan takarar Donald Trump ba, matakin dake cigaba da raba kan ya’an jam’iyyar watanni shida kafin zabe.
Donald Trump na ci gaba da haduwa da fushin wasu ya'an jam'iyyar dake danganta shi da mutumin da zai haifar da baraka a cikin jam'iyyar.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky