Dan Takarar Neman Shugabancin Amurka Ya Bukaci A Binciki Saudia

  • Lambar Labari†: 749655
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Democrate a kasar Amurka ya bukaci gwamnatin kasar da kuma majalisar

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Democrate a kasar Amurka ya bukaci gwamnatin kasar da kuma majalisar dattawan kasar ta gudanar da bincike kan irin rawan da kasar saudia ta taka a cikin harin 11-Satuban -2001M.

Bernie Sanders, ya bayyana haka ne a yau a lokacinda yake hari da tashar television na NBC. a yau Lahadi ya kuma kara da cewa idan an gano cewa kasar saudia tana da hannu a kissan Amurkawa a harin 11/09 suna da damar shigar da kara kasar saudia a cikin kotunan kasar.

Bernie Sanders, ya kara da cewa akwai wasu shaidu da suka tabbatar da cewa kasar saudia tana amfani da kudade wajen daukar nauyin ta'addanci a kasashen duniya.

Gwamnatin kasar Saudia dai ta bayyana cewa zata saida kadarorinta a kasar Amurka idan har majalisar dokokin kasar ta bude tattaunawa kan rawan da ta taka a harin 11/09-2001. Hakama shugaban kasar ta Amurka Barak Obama ya ce zai ki sanya hannu a kan duk wata doka ta binciken kasar Saudia da ta zo ofishinsa.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky