Iowa: Ba zan yi kasa a gwiwa ba - Trump

  • Lambar Labari†: 733090
  • Taska : bbc
Brief

Dan takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump, ya ce bai damu ba duk da rashin nasarar da ya samu a zaben fidda gwani na jam'iyyarsa da aka yi a jihar Iowa har sai ya kai ga nasara.

Sanatan jihar Texas ta Amurka, Ted Cruz, ne ya yi nasara a kan Mista Trump inda ya samu kashi 28 bisa dari na kuri'un 'yan jam'iyar ta Republican, yayin da Mista Trump ya samu kashi 24 bisa dari.

Mista Trump ya ce yana da yakinin cewa a karshe shi ne zai yi nasarar lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar Republic.

"Ban san waye zai yi nasara ba tsakanin Bernie da Hillary. Ban san me zai faru da Hillary ba don tana da matsalolin da suka fi na zaben fidda gwani," in ji Trump.

A hannu guda kuma, Hillary Clinton ce ta yi nasarar lashe zaben jam'iyyarta ta Democrat da shi ma aka yi a jihar Iowa din.

'Yan tawagarta sun ce babu yadda za a yi abokin karawarta ya kada ita.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky