Trump ya ji tsoron shiga muhawara

  • Lambar Labari†: 732206
  • Taska : BBC
Brief

Mai neman tsayawa takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican, Donald Trump, ya janye daga wata muhawarar da aka tsara za a yi ta gidan Talabijin din Fox.

Ya ce ya dauki wannan mataki ne saboda bai ji dadin wadda aka zaba domin ta yi alkalancin muhuwarar ba, wato Megyn Kelly.

Mista Trump dai bai sha ta dadi ba a wata muhawarar da Megyn Kelly ta alkalanta a watan Agustan bara, har ya yi wani furucin da ya janyo ka-ce-na-ce, cewa matar ta yi masa tambayoyi masu tsauri ne saboda tana fama da jinin al'ada.

Gidan Talabijin na Fox dai ya ce ba zai sauya alkalin muhawarar ba, wadda aka tsara za a yi a birnin Iowa a gobe Alhamis, kuma ita ce muhawara ta karshe, kafin a fara zabar 'yan takarar shugaban kasar.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky