Amurka za ta karbi ‘yan gudun hijirar Syria dubu 10

  • Lambar Labari†: 710179
  • Taska : http://ha.rfi.fr
Brief

Shugaban Amurka Barack Obama ya bayar da umurni kasar ta karbi ‘yan gudun hijirar Syria akalla dubu 10 amma sai a cikin shekara mai zuwa.

Mai magana da yawun fadar shugaban na Amurka Josh Earnest ya ce za a karbi ‘yan gudun hijira 1500 a wannan shekara yayin da sauran dubu 10 za a ba su damar shiga Amurka a shekarar badi.

A kowace shekara dai Amurka na karbar baki daga kasashen da ke fama da rikici akalla dubu 70, to sai dai tana dari-darin karba ‘yan kasar ta Syria.289


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky