Wannan shi ne kalaminsa na bainar jama'a na farko tun bayan da Netanyahu, ya yi nasara a zaben da aka yi ranar Talatar da ta gabata.
Shugaba Obama, ya ce Amurka, ta cigaba da yin amanna cewa, samar da kasashe biyu na HK Isra'ila da Palasdinu, ita ce hanya daya tilo ta tabbatar da tsaro da zaman lafiyar HK Isra'ila.
Mr Obama ya soki, kalaman ranar zabe na Netanyahu, inda Firaministan ya yi gargadin cewa tururuwar da Larabawa ke yi zuwa kada kuri'a, suna yi ne domin adawa da muradin HK Isra'ila.ABNA