Obama: Babu wani sabon abu a jawabin Natanyahu

  • Lambar Labari†: 674695
  • Taska : rfi
Brief

Shugaba Barack Obama ya ce babu wani sabon batu da Firaminstan Hk Isra’ila Benjamin Natanyahu ya gabatar a jawabin da ya yi a zauren majalisar dokoki ta Amurka. Yayin da ya ke mayar da martini kan jawabin, Obama ya ce Natanyahu bai gabatar da wani shirin da ya fi inganci kan yadda za a magance matsalar kasar Iran ba.

A jawabinsa, Natanyahu ya ce Iran makiyar Amurka ce. Kuma a cewarsa tattaunawar da manyan kasashen duniya ke yi da Iran dama ce na budewa kasar kofar mallakar makaman nukiliya sabanin kokarin dakile kudirin na Iran.

Natanyahu ya shaidawa Majalisar dokoki ta Amurka cewar ko da sunan wasa HK Isra’ila ba zata bari Iran ta mallaki makamin nukiliya ba, yana mai cewa idan duniya ta kawar da kai, HK Isra'ila ita kadai na iya daukan matakai.

Natanyahu ya ce ya san Amurka ba za ta juya wa HK Isra’ila baya ba.

Tuni dai Iran ta yi watsi da kalaman Natanyahu akan batun yarjejeniyar nukiliya tsakaninta da manyan kasashen Yammacin duniya.

Obama ya bayyana fatar sa na ganin an samu nasara a tattaunawar da suke da Jamhuriyar musulunci ta  Iran, amma Natanyahu ya bukaci Majalisar dokokin Amurka ta dakile duk wani yunkuri na sasantawa da Jamhuriyar musulunci ta Iran.

Rahotanni sun ce bangaren Jam'iyyar Republican mai adawa ne suka gayyaci Netanyahu ba tare da sanin fadar White House ba.ABNA


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky