Rasha ta jingine aikin gina hanyar shigar da Gas zuwa Turai

  • Lambar Labari†: 655456
  • Taska : rfi
Brief

Shugaban Rasha Vladimir Putin yace zai jingine aikin gina hanyar shigar da Gas zuwa Turai bayan gwamnatin Bulgaria ta toshe aikin ginin hanyar a karkashin teku. Shugaba Putin ya fadi haka ne a lokacin da ya ke ganawa da shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan a Ankara.

Shugaban Vladamir Putin wanda ke gudanar da ziyarar aiki a kasar Turkiyya yace Rasha ta jingine aikin gina hanyar shigar da gas zuwa Turai saboda rashin samun dama daga Bulgaria.

Putin ya fadi haka ne a lokacin da ya ke ganawa da shugaba Racep Tayyip Erdogon a ziyarar yini daya daya kai a Ankara domin karfafa alakar da ke tsakanin Rasha da Turkiyya, duk da cewa akwai sabani tsakanin kasashen biyu dangane da rikicin Syria da kuma Ukraine.

A ziyarar, shugaba Putin ya amince ya kara adadin gas din da Rasha ke ba Turkiya tare da rage farashin gas din da kusan kashi 3.

Rasha dai na neman gina bututun gas zuwa Turai daga kudanci ba tare da ratsawa ta Ukraine ba mai fama da rikici.

Kuma Putin ya soki hukumar Turai, yana mai zargin da yawun bakinta Bulgaria ta toshe aikin bututun man.

Putin ya ya yi gargadin cewa Rasha za ta rage yawan gas din da ta ke shigarwa Turai saboda matakin da Bulgaria ta dauka.ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky