Dansandan Da Ya Kashe Michel Brown Ya yi Ritaya daga Aikinsa.

  • Lambar Labari†: 655249
  • Taska : DPA
Brief

Dansandan da ya harbe matashi bakar fata wanda baya dauke da makami, wanda kuma wata kotu
a kasar ta wanke shi kan laifuffukan da ake zarginsa da shi ya yi ritaya daga aikin aikinsa.

Kamfanin dillancin labaran dpa ya ce Dareen Wilson dan shekara 28 a duniya yay i ritaya ne bayan da yaga sauran abokan aikinsa suna cikin tsaka mai wuya sanadiyyar tashe tashen hankula da suka bazu a birana ne da daman a kasar.

A ranar 9 ga watan Augustan da ta gabata ce Wilson ya harbe Michel Brown dan shekara 18 bakar fata Missouri na kasar Amurka , hakan ya jawo tashe tashen hankula a kasar, wanda ya kuma tilastawa hukumomi  gurfanar da shi a kutu. Sai dai kotun ta wanke shi bayan wani lokaci don abinda ta kira rashin wata hujja na hukunta shi. Hukuncin dai ya sake ruruta wutan rikici a kasar inda bakaken fatan Amurka suke ganin jami'an tsaro fararen fatar kasar basa masu adalci.abna


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky