Yan tawayen FARC sun sako jami'an sojan da suka sace a Colombia

  • Lambar Labari†: 655244
  • Taska : RFI
Brief

Shugaban kasar Colombia Juan Manuel Santos yace ‘yan tawayen FARC sun saki Janar din Soja tare da wasu Sojoji biyu da suke garkuwa da su.

Wasu na ganin wannan a matsayin wani mataki da ‘yan tawayen suka dauka na bude kofar tattaunawar sulhu da gwamnati.

Shugaban Colombia ya fadi a shafin shi na Intanet cewa ‘Yan tawayen na FARC, dake fada da gwamnatin kasar sun saki wani Janar din Soja da wasu sojoji guda biyu da suke garkuwa da su

Shugaba Santo yace nan bada jimawa bane Janar din na Soja da Sojin guda biyu zasu hadu da iyalansu, kuma dukkansu suna ciki koshin lafiya.

Wannan kuma wani mataki ne na bude kofar tattaunawar sulhu ta tsawon shekaru biyu tsakanin gwamnati da ‘Yan tawayen domin kawo karshen rikicin ‘Yan tawayen da aka shafe shekaru 50 ana yi a Colombia inda Mutune sama da 220,000 suka mutu. 

A watan Nuwamba ne ‘Yan tawayen suka cafke Sojojin na Colombia, tare da babban kwamandan Sojan kasar Brigadiya Janar Ruben Alzate da ke jagorantar yaki da ‘Yan tawayen.

Wannan matakin na sako sojojin da ‘yan tawaye suka yi, zai sa bangarorin biyu su koma teburin sulhu a birnin Havanan kasar Cuba, bayan sun dakatar da tattaunawar tun karshen 2012.ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky