Hannun Da Amurka Take Da Shi Cikin Dagula Lamurran Tsaron Afghanistan

  • Lambar Labari†: 640209
  • Taska : http://hausa.irib.ir/
Brief

A jawabinsa na karshe a matsayin shugaban kasar Afghanistan, shugaban kasar Afghanistan din mai barin gado Hamid Karza'i yayi kakkausar suka ga gwamnatin Amurka da bayyana ta a matsayin kanwa uwar gamin matsalar tsaro da kasar take fuskanta. Har ila yau a jawabin nasa da ya yi fadar shugaban kasar a jiya Talata shugaba Karza’in ya ce Amurka da Pakistan su ne ummul aba’isin din ci gaba da yakin basasan da ke gudana a kasar tasa, kamar yadda kuma ya ja kunnen sabuwar gwamnatin kasar da ta yi taka tsantsan cikin alakarta da Amurka da kasashen yammaci.

Shugaba Karza'i ya ci gaba da cewa daya daga cikin dalilan da suka sanya yakin kasar Afghanistan din yaki ci ya ki karewa shi ne cewa tun da fari ma Amurkawa ba suna son tabbatar da sulhu a kasar ba ne, face dai suna da tsari da kuma manufarsu ta musamman da suke son cimmawa a Afghanistan din; don haka ya ce matukar dai Amurka da Pakistan ba sa son ganin an samu sulhu da zaman lafiya a Afghanistan to kuwa ba za a taba samu ba.

 

Wannan dai ba shi ne karon farko da shugaba Karza’in yake sukar siyasar Amurka a kasar tasa ba wacce ta shigo da takewa da batun fada da ta’addanci. Tsawon zamanin mulkinsa wanda ya faro tun daga shekara ta 2004 zuwa 2014, shugaba Karza'i yayi kokarin ganin an magance matsalar da kasar Afghanistan din take fuskanta ta hanyar ba da hadin kai ga gwamnatin Amurkan, to sai dai kuma hakarsa ba ta cimma ruwa ba lamarin da ya sanya shi yanke kauna daga siyasar Amurka musamman a shekarun karshe-karshe na mulkin na sa.

 

Sabanin da ke tsakaninsa da Amurkawan dai ta kara fitowa fili ne bayan da ya ki amincewa ya sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro tsakanin gwamnatinsa da gwamnatin Amurka da nufin ci gaba da barin dubban sojojin mamayan Amurkan a kasar. Shugaba Karza’in dai ya ci gaba da bayanin dalilansa na kin sanya hannu kan wannan yarjejeniya saboda yana ganin Amurkan a matsayin ummul aba’isin din rashin tsaron da kasar Afghanistan take ciki ne. Don haka ne ma ake ganin wannan suka da ya yi wa Amurka da Pakistan cikin jawabin nasa na karshe da kuma kiran sabuwar gwamnatin da ta yi taka tsantsan a matsayin ci gaba da irin wannan kai ruwa rana da ke ci gaba da wanzuwa tsakaninsa da Amurkawan ne wanda yake ganin ci gaba da zamansu a kasarsa a matsayin babbar barazana ga kasar.

 

Ko shakka babu daya daga cikin batutuwan da sabuwar gwamnatin kasar Afghanistan din za ta gada wacce kuma za ta ci gaba  da zama alakakai cikin alakar kasashen biyu shi ne batun yarjejeniyar tsaron da Amurka ta gabatar wacce shugaba Karza’in ya ki amincewa da ita. Shugaba Karza’in dai ya ki sa hannu kan wannan yarjejeniya da barinta ga gwamnatin mai zuwa wacce ita ce take da wuka da nama a hannunta ko dai ta amince ta sa hannun ko kuma ita ma ta yi watsi da ita.

 

Jim kadan bayan kafa sabuwar gwamnati a Afghanistan bayan yarjejeniyar raba madafan iko da aka yi tsakanin ‘yan takaran shugabancin kasar biyu Ahmad Ghani da Abdallah Abdallah wanda kowanensu ke ikirarin lashe zaben ne, gwamnatin Amurka ta sake taso da wannan magana na sanya hannu kan yarjejeniyar tsaron lamarin da ke kara sanya shakku cikin zukatan al’ummar Afghanistan din dangane da manufar Amurka cikin son ci gaba da zama a kasar.

 

Masana al’amurran yau da kullum dai suna ganin, duk da cewa sabbin shugabannin Afghanistan din wato Ashraf Gani da Abdallah Abdallah a lokacin yakin neman zabensu sun yi alkawarin sanya hannu kan wannan yarjejeniyar, to amma da wuya a ce sabuwar gwamnatin za ta yi gaggawa cikin sanya hannu kan yarjejeniyar musamman idan aka yi la’akari da bangaren yarjejeniyar da yayi magana kan wajibcin sanya rigar kariya ga sojojin Amurkan da suke kasar daga gurfanar da su a gaban kotu kan duk wani laifin da za su yi lamarin da ke ci gaba da fuskantar suka daga wajen al’ummomin kasar. ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky